23.5.10

munafuncin aku


A makonni kadan da suka gabata ne yan Najeriya kowa ke tofa albarkacin bakinsa kan wani ango da wata amaryar da aurensu yafi kowane aure shahara a Najeriya. Wannan angon ba wani bane face Ahmad Sani yariman Bakura wanda ya shekara takwas a matsayin gwamnan jihar zamfara , sannan a halin yanzu yake matsayin sanata mai wakilcin daya daga bangarorin jihar . Lokacin mulkinsa Ahmad sani ya zama zancen daukacin mutanen Najeriya daga addinai , bangarori da harsuna daban-daban wasu na yaba masa wasu kuwa na kushe shi kan yunkurin da yayi na tabbatar da shari’ar musulunci a jihar da Allah ya bashi riko , wanda yanzu haka gwamna yana matsayin sanata sakamakon zaben daya lashe ba tare da wani magudi ba.

Babban tabon da wannan gwamna yake dashi a wajen kasashen waje da wasu kungiyoyi masu riya kare hakkin dan adam da wasu masu riya fafutukar Islama shine kokarin dawo da martabar dokokin Allah, saboda gaba da addinin , wasu kuma saboda ba jagoransu bane ya samu nasarar hakan . wani na kusa dashi Malam Ibrahim Wakkala a wata laccar daya mana ya sanar damu cewa a kasar Ghana wasu mutane sun masa alkawarin makudan dalolin Amurka don ya janye wannan niya tasa amma hakar su bata cimma ruwa ba .

Daga cikin nasarorin da wannan mutum yaci shine ya sanar da mutanen kudancin Najeriya me ake nufi da kalmar Shari’a wanda kafin hakan basu santa ba , sannan ya kara kaimi wa kotunan shariar musulunci don kada suyi kasa a gwuiwa wajen zartas da hukuncin Allah koda kuwa yanke hanu ne ko jefewa , hakan ya yunkurar da jama’ar sauran jihohi har suka tursasa gwamnoninsu zartarwa ala tilas.

Idan muka ajeye son zuciya da son shahara zamuga cewa shari’ar musulunci wani kwas ne wanda ake karantarwa a jamio’in kasar nan sannan aka ba lauyoyi damar kafa hujja da tanadinsa a gaban alkali, to meye laifi don wani yayi kokarin tuka shi gaba? Toyau Allah ya kawomu wata rana wanda abokan gaban yarima suke ganin cewa zasu rama tabbatar da shari’ar da yayi .

Bari in gaya wa mai karatu cewa wadannan kungiyoyin kare hakkin dan adam , mata da kananun yara akwai munafunci cikin aikinsu tunda basu taba zuwa gidan karuwai don su kama matan dake kasa da shekara sha takwas 18 sun dauki wani mataki a kansu ba , sai kawai don sanata yarima ya auri mace aure na sunna ,ba zina ba , ba kuma fyade ba da sadaki a kuma babbban masallacin Najeriya a gwamnatance suna ta daga jijiyar wuya suna kashe tituna. Wani abun ban dariya abun Hajiya Ramatu Bala Usuman taji kunyarsa shine wannan amarya bata ce muku bata son angonta ba , ba kuji labarin cewa auren dole ala mata ba , kuma baku san takaimaiman shekarunta ba , wata kila baku san sunanta ko kunga hotontaba , kawai a jita-jita kun tada zanga-zanga don aiki bai ishe kuba .

Zan so in waiwayi makalar wani marubuci Mahmoon Ahmad Baba mai taken AKAN BAR HALAS DON KUNYA wanda ya rika kiran wannan amarya YAR KWAILA , amma ba mamaki bai sani bane , amma a matsayina na wanda yaje kasar masar har sau uku kuma yasan irin girman larabawa zan tabbatar maka cewa balarabiya yar shekara sha uku zata zuba da yar shekara ashirin da uku a gummu ko ma fiye .

Ban ji labarin wadannan kungioyi sunyi wata zanga-zanga ba sanda akai wa malam jafar kisan gilla , in sun ce su masu kare hakkin dan adam ne , to shi malam kiyashi ne ? in kuma masu kare hakkin mata ne , to ko shi baida mata ne ? ko sanadiyar rashinsa rayuwarta baza ta gurgunta ba ? , in masu kare hakkin yara ne , to shima ai yana da yara , ko ba irin wadannan yaran ake karewa ba ? abunda ya baiyana shine wadannan kungiyoyi ana amfani dasu ne daga kasashen waje don tozarta musulunci da bakanta shi , basu da wani abun cewa sai wanda aka sasu suce kamar aku kuturu , shi yasa nake tare da Ado sale kankiya inda yake cewa ‘‘ abunda na fahimta daga kwakwazon kungiyoyi shine kasashen turai dana Amurka dana yahudawa da suka sa addinin musulunci a gaba ne kawai suke amfani dasu domin su cimma burinsu na rusa addinin Islama da musulunci ’’

Duk wani bita da kulli baza a iya mancewa da yarima ba a bangaren ciyar da Shari’ar musulunci gaba ba , don kuwa duk sanda aka fara da shehu usumanu Dan hodiyo za’a yi ta gangarowa har sai an fadi akan Ahmad sani , kafin wani mujaddadadin ya biyo baya .

Allah ya rabamu sharrin masharranta



Auwal Muhammad Abdulkadir
alkalami1@yahoo.com
+2347030703318
Bauchi
www.alkalami.blogspot.com

26.9.09

Thursday, May 29, 2008
روايات إسلامية

ثورة النساء

قصة طويلة





عبد الودود يوسف








- 1 -



- 1 -



Rana ta kama hanyar faduwa , a daidai lokacin da al,amari yake kara yamutsewa tsakanin samaruka uku , burjeh a bagare , totman da brija a daya bagaren , Samora kuwa tana bangaren dan,uwanta tana tallafamasa da duk abunda zata iya don galaba akan biyun , a karshe dai abunda take tsoro ya faru , don kuwa koda kwallo ya fada ragarsa sai ya ciro wuka ya farka kwallon , sukuwa biyun suka haura kansa , shi kuwa ya una musu wuka yana da baya da baya , ita kuwa Samora tana razane ta san komi zai iya faruwa , nan da nan burjeh yai gaggagawa izuwa ga wani dutse don ya rusa masa kai , nan take Samora ta sha gabansa do kar ya cimma muradinsa , shi kuwa ya kubuce yadanyi gudu wanda baifi taku hudu ba sannan ya tsaya ya sami daidaituwa ya maida hanu mai dutsen baya sannan ya harba dutsen , amma a banza don kuwa burjeh ya sheke ya bar kanwarsa ta shaya abunda ya jikawa abokan fadansa.


Totman yayi iya kokarinsa don ya cimma burjeh , shi kuwa birjan yayi kan Samora , nan take tace ‘ ‘ ka sani fa ba dani kake fada ba da wana burjeh kake yi ‘’ shi kuwa bai ko hankalta da maganarta ba , ya kamata ya yarfa tada kasa yana cewa ‘’ sai na yaga rigarki kamar yadda wanki ya yaga mun kwallona , ta samu ta tashi tana kata daidai karfinta. Ana haka sai Totman ya kamota ta baya burjeh kekketa tufafinta , hakan ya fusata ta matuka wanda tai kai msa yaga kamar zakanya , tufafinta sabo ne , gashi mahaifinta bai saya ba said a ta shekara tana rokonsa


Duk fa abuda ya faru ba wanda ya kubuce ido Burjeh ,wanda Samora ta yi kiran neman taimakonsa , amma matsoracinka bai waiga wa bukatarta ba , har ta yanke tsammani , ya barta ta warware abu day a kulle , haka ya kara mata jarunta da fusata hart a sami damar yasar da Birja a kasa , ta hakansa kenan sai abokinsa Totman yazo ta baya ya tunkudeta a kansa suka gudu.
Ta tsaya tana nishi , tana kallon sabbin kayanta a kekkece , sai tayi murmushi nasara , kawai sai taji fadowar wani babba dutse a kanta , ta fadi a kasa ta bar duniya na wani lokaci

Koda wata ya karaso sai yaga hali da take ciki sai yace a ransa ‘’ da alama Samora ta mutu ‘’ ya maza ya koma gida tsoron kada babasu ya haushi da fada


Can sai Samora farka da suman da tayi , taga duhu ya lullube duniya ,ta mike tana so ta tafi gida amma rauninta bai bata dammar hakanba , saboda jinni sai kwaranya yake daga kanta taji kanta kamar wani dutse , tana ganin abubuwa suna ba ware ba suna shiga cikin juna , sai tayi niyar ihu ta kasa , sai ta fara jajikita a kasa tana kokari isa gida kada jiita ya tsiyaye gaba daya tana cewa ‘’Burjeh yayana kazoo ka taimakeni‘’ a daidai lokacinda shikuwa yake minshari a kan gadonsa

A wannan mawuyacin halin ne Samora ta ji dariyar mahaifiyarta a nesa , ta hagota tana kwanciya jikin abokinta shatran shi kuma yana rungumeta da gasket sai tace da babbar murya ‘’ Mama ki cece ni , nice Samora ‘’ ta juya bata ga kowa ba sai ta cigaba da sunbantar Shatran , da alama bata fatar wani shagaltarda ita ga barin sunbantar abokinta , saidai kuma wannan kira na Samora ya maimaitu , sai abokita Shatran ya juya ya shiga cikin duhun , mahaifiyar samora kuwa sai kiransa take ’’ kar ka kula wannan shegiyar ta katse mu , makaryaciyace ‘’’ koda ya ganta cikin jinni sharkaf sai yace ‘’ haba saninth yarinyar nan da gaske takeyi mana ‘’ koda taga fushin abokin nata sai ta gaggauta zuwa gun , Abokita shatran ya dauketa ya wuce mahaifiyar samora tana binsa abaya har suka isa ga motarsa ya shige da samora , saeth ma ta shiga kamar dole suka tafi asibiti don taimakon gaggawa

Kwanaki biyar sun wuce samora tana sume , a rana ta shida neta bude idonta taga mahaifinta a takure a dungun daki mahaifiyarta ma tana takure a daya dungun ,
-
- A daidai wannan lokacine Shatran masoyin mahayaifiyarta , da franso masoyiyar mahaifinsa suka karaso jikin gadonta suka mata murmushi , mahaifanta kuwa da alama fushi ne ke tafarfasa a zuciyarsa , samora kuwa mamakin hakan ne ke kwaranya a ranta . ana haka sai wani mutum ya shigo da wata takarda a hannunsa yace wannan takardar cajin da muke wa samora ne muna fata zaku biya zuwa gobe saboda zamu sallameta gobe , ana haka sai betnam baban samora ya dauko takardar ya nazarinta yace ‘’ faranki dubu da hamsin kawai ‘’ ya zunbura baki , ya waigi samora yana cewa ‘’ shegiya ba abunda kike jawo mun sai bala’I , ina ma ki mutu in huta ‘’ sai samora ta fashe da kuka tana cewa ‘’ aiya baba ina ma na mutu don kar in dameka ‘’
Borje yace yar iska ita ta tsokani totman da berjan su kuwa suka kwada mata dutse , maman tace ‘’ amma kana da masaniyar sun mata rotes kuma ka tafi ka barta? Hakan ya sa burjeh ya dan dimauce ya rasa me zaice , ita kuwa samora sai shishshikewa take hawaye yana kwaranya daga idanunta . da ganin haka sai shatran samarin mamanta ya fice , ita ma faranso budurwar babanta ta tafi. Sai baban yace ‘’ to ai sai kiya kudin jinyar yarki don ina cikin karayar arziki

‘’ nan take ta rike ta dawo kamar wata damisa tace ‘’ don me zan biya kudin jinyar yarka , bazan biya ko faranki daya ba , ina kudin da kake facaka wa karuwai dasu , shima ya mayar mata cikin tsawa ‘’ ba ruwanki da irin rayuwar da na zabawa kaina ya fita daga asibi tin yana cewa a ransa ai baza ta iya fita ta bar yarta a wannan yanayin bata biya kudin jinyar ta ba
Saneith ta gaura wa danta mari tace ‘’ mu tafi gida , dolensa ya dawo ya biya wannan kudin’’ . harta fita sai ta dawo ta dauki takardar cajin ta rubuta 9 b street
Wannan shine adreshin baban samora , atuntubeshi duk sanda ake bukatar kudin jinyarta, daga nan kowa yasulale ya barta cikin fargaban rashin sanin makoma da madafarta , amma abunda tafi tsammani shine zasu rufe tane sai kudinsu ya nuna a hannunsu , sautin kyauren dakin ne ya yanke mata tunaninta ,inda wata mai reno ta kawo mata abinci , mai renon tai mamakin meye dalilin kukan Samora , sai ta tambayeta ko lafiya ? ina ne yake miki ciwo ? ina mama da baba ? dajin haka sai kuka ya karu , mai renon ta ruga da gudu da kira likita , da zuwansa sai ya bata wasu kwayoyi , tayita barcin da bata so farkawa daga shi ba .







- 2 -



2

Samora gari yawaye mata , bata ga mahaifiyarta ko mahaifinta ba , sai akawu ya shigo yana cewa ‘’ me yasa suka tafi suka barki ba tare da sun biya ba ? Samora tace ‘‘ zan biya ku kudinku da kaina! ’’ hakan yaba akawu dariya yace ‘‘ to biya mu yanzu ’’ tace ‘‘ sai na warke in yi aiki in biya ku ’’
A’ina zakiyi aikin ?
A duk inda kuke so .
Yayi kyau, zan tambayi manaja ko za’a sami wani aikin da
zaki iyayi , kuma ban so ki dami kanki don ke karamar yarinya ce ’’
Nan take ta katseshi da cewa ‘‘ a’a niba karamar yarinya bace , yau shekaruna sha uku don hakan a wuci ace mun karama ’’
Yace ‘’ shikenan , duk yanda kika ce daidai ne ’’

Bayan wani dan lokaci sai wani santalelen saurayi ya shigo dakin jinyarta , ya tambayeta kece Samora ? wani iri da wani irin aiki kika iya ? sai ta bashi amsa da cewa : na iya wanki , guga da goge gilasai , sannan ina da kwazo matuka , don ni nake zuwa na daya a ajinmu , zaka iya saka ni ko wani irin aiki , kuma zaka ga yanda zan yishi yanda ya kamata , wannan samari ya mata wani kallo dake nuna cewa zata fada tarkonsa , yace yayi kyau , zaki mana gugan tufafi na tsawon wata uku maimakon kudin jiyarki , zaki kuma ci abunda sauran masu aiki sukeci , za kuma mu baki makwancin da ya dace dake , kin yarda ? ta kada kai tace na yarda , ya bata wata takarda ta sa hannu , ya fita . wannan abunda ya faru ya sa samora ta zage taci abinci da kyau , ta kumayi barci mai nauyi , ba mamaki , saboda wata damuwa da ta tukuikuye mata zuciya ta kawu . amma duk da haka Samora tunanin da ya fado mata shine ‘’ yanzu kenan zan bar makaranta , zan fara aiki tun yanzu , banda sa’a kamar sauran kawayena da suke ci gaba da karatunsu , zan fara aiki kafin shekara hudu , amma ba komai , zan saukakewa mahaifina da mahaifiyata wannan nauyin mai girma ’’ taja dogon nunfashi ‘‘ zan tara kudi zan sayi gida da mota , in sami miji kamamme wand azan Haifa masa ‘ya’yan da zasu rayu a dausayin zuciyata.

Zuwan wadannan abubuwa a kwakwalwarta ya bata mamaki , sai ta tambayi kanta ‘‘ shin zan bar wana , mahaifina da mahaifiyata ? , zan bar gidanmu da makarantarmu ? take kuma sai ta mayar wa kanta martani ‘ ‘ dole inyi aiki don zama ‘yantacciya , in nemi na kaina ” ta manta cewa abunda zai dauru akan shekarunta baikai ya kawoba . wata Nas ta shigo cikin damuwa ta tambayeta “ da gaske kin kudiri aniyar aiki a nan? ” samora tai murmushi tace “ e! so na ke in nemi nawa da kaina ” sai kwalla ta taru a idon wannan mata tana cewa “ samora ina miki gargadi da ki tuna cewa ke karamar yarinya ce ki koma gun mahaifanki ki mori kuruciyaki a gabansu me yasa kike gaggawar gurbata rayuwarki ! ” furucin wannan mata ya kullewa Samora kai , meye abun gurbata rayuwa a aiki tsakanin wadannan mutane ? , batare da wannan mata ta lura da rudewar Samora ba sai tace “ in dai don kudin jinya ne zan biya miki , amma gaskiya ina jiye miki aiki anan , don kuwa yanzu haka suna kitsa yanda zasu raya dare dake , na kuma gansu da idanu , na jisu da kunnena , ki koma gida azabar da kike sha a gida bazata kai wacca zaki fuskanta a wannan asibiti ba ” bata sami amar kaiwa in take nufin kaiwa ba saita fashe da kuka , Samora tai maza ta fara share mata hawaye tana tambayarta “ me ya faru ? waye ya bata mata , don Allah in nice kiyi hakuri bada nufi nayi ba ” ta kara share hawayenta da kanta tana cewa “ kina da ‘yancin yin abun da yayi miki zaki , kawai dai nasiha ce na nufa ”” sai ta fice .
Samora ta shiga rudani dangane da batun Nas dinnan ta kuma tambayi kanta me ake nufi da “ raya dare” a wannan asbitin ? don me zan koma gida alhalin anan zan sami kudi kuma in zama ‘yantacciya ? amma kuwa gashi nas dinnan mai gaskiya ce , da alama kuma tayi niyar biyan kudin daga aljihunta , da badon samora tanada kawaici da kara ba , bata so wani ya biya mata koda faranki daya ne , tace a ranta “ koma yaya ne zanyi aiki na tsawon wata uku ne kacal , in ga me zai faru , in aikin ya dace in ci gaba in kuwa ba haka ba in koma gidan mahaifa na ” likita sai ya shigo tare da wannan Nas din , samora taimata wata ‘yar fara’a , ita kuwa Nas tai mata kifcen cewa ta boye alakar dake tsakanin sub a tare da likita ya sani ba hakan ya ba Samora mamaki amma duk da haka sai ta zartar da umuninta
Likita ya warware bandejin da ke kanta , yatabbatar cewa raunukan da ke kanta sun warke yace mata “ ina taya ki murnar warkewa , bayan kwana biyu zaki koma gida , me kike gani ? tace kamar yadda ka gani , , sai cigaba da hada kayan aikinsa yana cewa “ me ya faru banga mahaifiyarki ko mahaifinki ba ? ” bata bashi wata amsa ba , sai ya ciga ba “ko da yake mahifa sau da dama sukan shagaltu da wasu hidimomi kamar aiki , neman kudi , neman jin dadi da kuma……. Raya dare ” abun day a bashi mamaki shine fadinta “zanyi aikin wata uku maimakon kudin jinyata ” har hakan yasa yayi tsammanin ko bata da iyaye ne , ya fita yana sake-sake Nas din kuma tana bakin cikin Samora bata yarda da ra’ayinta ba , ita kan Samora tana cikin farin cikin sabuwar rayuwar da ta shiga .



- 3 -






- 4 –






- 5 -






- 6 -






- 7 -






- 8 -










- 9 -





- 10 -





- 11 -






- 12 -








- 13 -



.



- 14 -






- 15 -











- 16 –





- 17 -






- 18 -






- 19 -





- 20 -






- 21 -


mamaki ya kama jabon matuka lokacinda sonda ta nemi ya barta ta fice a daidai karfe sha daya na dare, saiyace mata " ina zaki cikin wannan kankarar , kowa yana barci" tace :" ina tsammanin na sama sharadin zaka barni in ci gaba da aiki na da samora duk sanda na so" ya nunfasa " gaskiya ne .. to amma me za kuyi a wannan lokaci " tace masa " karka yi hanzari zaka sami labari " ta hau motarta ta wuce
wata mace sharan titi dan firgita da ganin duhu duhun mutane uku kamar fatalwu suna kusantota , amma dai duk da haka ta ci gaba da tura amalanken sharanta da kyar samoda kankarar da ta cike tituna, daga karshe dai ta fahimci cewa 'yan'uwanta mata ne , daya daga cikin matan ta karbi amalanken,

samora ta fara tambayar ta

" shekarunki nawa madam!"
" shekara sittin"
kan wannan tsohuwa duk yayi fari saboda kankarar da ke sauka kanta


" nawa ake biyanki"
" faranki arba'in a wata" ta kara da cewa " 'yata wannan albashi yayi kadan matuka , to amma ya zamu yi, yanzu haka ina biyan kudin haya dakin kwana kuma ina bukatar magunguna "
samora ta nunfasa " ba shakka bai albashinki bai taka kara ya karya ba ,ya kamata ya karu don kiyi rayuwa mai dadi "

tsawon sao'i nawa kike yi a aikin?"

sa'a sha biyar "

tirkashi da wannan tsufa naki'' samora tace

" to 'ya'ya nawa gareki ? "

" mijina ya gudu ya barni lokacin da na yankwane kamar fure bayan kamshi da launin ban-sha'awa , da ni kyakkyawa ce kwarai, ina da masoya da dama , amma yanzu duk sun koma ga watata da na girma, haka mijina ma , 'ya'yana kuwa ni da ubansu maka ringa takura musu don su gaji damu su guje mu , mu kuma mu samu hutawa da cinsu da shansu da suturarsu, amma lokacin budurci na zubar da jarirai biyu da na dauki cikinsu daga wani , wadanda na haifa da aure su uku ne , macen ta kashe kanta saboda rashin kyakkyawan fata a rayuwa da kasa jure aikin karfi don ciyar da kanta , yanzu haka ban san kabarinta ba , mazan kuwa daya matuki ne , gudan kuwa babban dan kasuwa ne , sukan turo min da wasu yan kyaututuka ranar idun uwa , amma ba abunda 'yan kyaututtukansu ke toshe mun , don haka ala dole in fito inyi aikin karfi "

Samora tace " to idan baki fito aiki ba saboda rashin lafiya wake maki hidima "

sai tace cikin kuntata " babu ! shiyasa na gwammmace mota ko jirgin kasa ya markade ni , kuyi hakuri kubar ni in cigaba da aiki na kar su kama ni na tsaya zance "

ba ki ganin Sonda zata karasa miki aikin " inji samora

tsohuwar tace " sonda kawar samora ! ku isar mun da sakon gaisuwa ga Samora , mai neman 'yancin matan faransa gaba daya , zukatanmu na tare da ita " ta kara da cewa da ace ni macen aure ce kuma mutan faransa sunki yarda da farkoki da yanzu ina tare da yaran da mijina da wadatar dukiya da ta zuciya, ni babban fatana in sami mai bisneni bayan na mutu , kai Allah wadaran wannan gari ..... da ace zanyi ido hudu da Samora dana ce mata ta ya kamata cikin kiraye-kirayenta ta nemi akashe duk wata farka da dadiro , saboda sune masu kashe al'uma da ranta " .

koda SONDA mata nuni da cewa ai tana gaban Samora ne sai tai tsa rungumeta tana kuka....''
Samora ta rarrashe ta ya yambayeta " idan muka ce kiyi yajin aiki don ki sami 'yancinki da kulawa za kiyi? sai tace in gaya maki gaskiya samora ko makami kika ce mu dauka don yakan mujiramai zamu dauka , don da gadon wulakanci gwamma gadon mutuwa
cikin wannan daren dai samura da mabiyanta sukai ta kai kawo cakanin maikata sannan suka shirya irin wannan bincike a sauran biranen faransa

A mako guda komitin samora ya tattara sakamakon binciken da suka gudanar sai sakamakon ya kasance :

# galibin mata masu aikin karfi munanane ko tsintattune ko gajiyaiyu
# mafi karancin lokacin aikinsu shine sa'a sha uku
# Abun da ake basu baya biya musu kananun bukatunsu na rayuwa
# mafi yawancin wadannan mata sun fito ne daga gidan da ba tsayaiyen aure
# jama'a suna kara muzgunawa mata saboda bukatuwar matan zuwa garesu
# dukkanin matan shirye suke da yin zanga-zanga ko yajin aiki ko duk abunda zai dawo musu da 'yancinsu
# kuma dukkansu suna shirye da suyi kafar angulu da karuwanci , suna kuma neman dokarda zata hukunta mazinata

Koda jin wannan sakamako sai Samora ta buga teburi tanacewa " dole mubi hanyoyin da zamu karbo darajar da wasu suka kwace mana koda kuwa da tashin hankali ne in ta kama "

Sonda tace " wannana gagarumin aiki yana bukatar wadanda basa aikin komine""

suka zauna don sawa wannan kungiya da suke so ta tattara dukkan matan faransa suna " kungiyar yantadda matan faransa "

suka tashi a taron da azamar sadaukar da kai ga wannan manufa tasu .









- 22 -




Koda faransawa suka wayi gari sai suka ga duk an lillika sanarwa cewa " samora tana kiran dukkan mata da su yi rijista a rassan kungiyar 'yanta matan faransa , saboda hakan shine zai bada damar nunawa mazan faransa kimar mace a matsayinta na uwa ko yar'uwa ko matar aure mai aiki ko maras aiki "

lokaci daya rassan kungiyar suka karbi mambanci mata dubu ashirin , kowa cikinsu ta biya faranki dubu dari kudin rijista

Samora tace yanzu zamu fara aiki tukuru ! wazai sadaukar da kansa ?

Matan suka " samora ! kece kawai zaki iya wannan aiki , mace kamar maza

tace " da sonda da Hamony , jabon da mahaifina kuma zasu kafa kungiyar maza mai tallafa mana " sannan a kowani reshe zamu nada jagora kowace jagora ya wajaba ta sanya wando mai kauri wanda bai kwantuwa sai da jibin goshi , ko tufafi mai rufe musu jiki gaba daya , don su gwadawa kurayen faransa cewa basu yarda da ganin jikinsu ba , kuma hakan bata sabuwa saiga mazansu na aure "

Sonda tace me yasa bazaki farlantawa kowace manba hakan ba ?

Samora ta kalle matan tace " wannan ya rage nasu "

koda suka ji irin ba'a da jagora tayi sai sukai ta mubaya'a kan sa wando mai kauri , don haka samora tasa aka akaita dinka wandunan a kowane reshen ofishi ana matan na saya farashi mai rangwame.
Mutan faransa sun kasa gaskata abunda idonsu ke gane musu na wadannan wandunamasu fadi dake rufe dirin jikunan matan , Har Mr Andrew ya dimauce sai sunbatu yake don matan asibitinsa duk wannan igiyar ruwa ta jasu , bugu da kari ga Jabon yana mara musu baya.

'' Allah wadaran Samora " in jishi " tana so ta tilastawa masa subi ra'ayoyinta , yaza ace bazamu kwanta da wacca muke so ba , kawai sai wata ta zo ta ta takaitamu ga mace daya ?, ya kamata maza su daukin matakin gaggawa don ganin bayanta "

Yana cikin wannan sake-saken sai Sonda ta shigo tace " barka da war haka " bata mika masa hannu ba , ya amsa cikin murmushi ,bata ma san ko yanayi ba , ta mika masa wata takarda dake hannunta , ya karba ya fara karantawa sai ya katse karatun yace " me zaisa ki bar aiki dani Sonda ?",
cikin izgili tace "don in baka dama ka dauki sakatariyar da zaka ringa bata dare da ita"
shima ya mayar mata a harzuke " to laifi ne bata daren da wacca nake so ? bace mun daga gani , na koreki ke da mijinki Jabon , ba zan iya jure cin mutunciba "

" ai da ka karasa karanta takardar da ka fahimci cewa ni dashi muka rubuta wannan takardar neman barin aikin"

maza ta fice ta barshi cikin damuwa r yanda zai fitowa wannan masifa dake neman dulmuyar da asibitinsa , Ashe kadan ya gani.

Koda Sonda ta fito daga ofishin M.r Andrew sai tai rada a kunnen wata ma'aikaciya , ita ma tai wa wata , nan da nan sai kuskus yai ta zagayawa , kafin rubu'in sa'a sai sai matan suka yi cincirindo , sai SONDA ta fara huduba :
'' mu wawaye ne idan muka yarda da albashin da bai taka kara ya karya ba ko muka yarda tsawon lokacin aiki , ko kuwa muka yarda maza su debe kewarsu da ganin tsiraicinmu , don hka muna da zabi biyu , ku muzama wawaye ko matan aure masu mutunci !"

samora tana sa aya sai wurin ya rude da tafi da sowa , ta sauko suka tafi da mijinta. matan kuwa kowa ta koma gurbin aikinta.
jim kadan sai Mr Andrew ya fito ran gadi, sai riski wata budurwa tana goge kayan ungozoma da likitoci ,ya mika mata hannu don su gaisa har tayi niyar ki amma dai ta mika masa ta zame hannunta da sauri , yace mata " aikin ki yana tafiya daidai" sai tayi murmushi , ya kara da cewa " gashi kuwa ke kyakkyawa ce " sai fuskarta ta turnuke da fushi tace cikin gatse" hakadai hakadai , kina da kyau , ki cire wannan mayafin , kizo mu kwana tare , daga karshe ka barni da yaro shege , in kuma na nima masa hakkinsa ka kore ni ? faufau bazata sabu ba" koda yaji wannan martani mai kaushi sai ya yi gaba da sauri ita ko ta mai dariyar cin nasara.
ya karasa gun wasu yan mata yace wannan wando naku yana da kyau " sai guda tace " ba shakka , amma baza mu yaye shi ba sai ga mijin aure" yace to a ina zaku sami mijin aure" tace " idan mata suka bar zubar da mutuncinsu ga dadiro" wata ma tace " yanzu baka da da da yake amsa sunansa tare da naka , wanda wata ran zai zama gwamna ko waziri {minista} mashawarcin shugaban kasa ."
haka yai ta kewaye-kewaye don yasa mi wacca zai kwana da ita , amma hakan yaci tura ,
don haka ana tashi aiki sai yan matan sukai kicibis da wata takarda like kan allon sanarwa , suka taro suka karanta abunda ke kai sai suka ga an ributa " daga yau ba yau ba , kar wata ma'aikaciya ta saka buje , saboda yana kazar kazar wajen aiki , duk kuwa wacca ta kuskura ta sanya , ta tabbata ta bar aiki kenan"
Hakan ya sa kowa cikinsu taji tsoro , wadanda dama basu saba suka fara izgili da tsokana ga wadanda suka sa , wasu suka ce gaskiya gobe zasu tube saboda karsu rasa aikinsu.

ita kuma Samora tana aiki tukuru don shawo wannan matsala dake neman barkewa
ta tambayi sonda " ma'aikata nawa ne a asibitin Andrew?"
Sonda tace " su dari ne"
Samora tace " yayi kyau , in ya koresu shi zai shiga matsala , mu kuma muna shirye da mu sama musu aiki da albashi mai tsoka"

cikin wannan daren samora da sonda suka nufi asibitin Andrew don su tattauna da matan da aka kora saboda sun ki tude wandunansu.




23
Koda likitoci suka shafawa sanit ruwan sanyi a fuska sai ta farfado da ambaton samora kamar dama shine makale a bakinta kafin ta suma, wata daga cikin likitocin tace ai samora tana kurkuku, kuma za'a gurfanar da ita a gaban alkali nan bada jimawa ba.
nan take sanit ta firgece da sunbatu " wa ya isa ya taba mun 'yata , ku nuna mun hanyar kotun"

sudai likitocin kowa ya tsaya cikin mamaki yana zubawa kudurar Allah ido , sai ta sabi kayanta ta fice saura kadan wani mai babur ma ya bugeta.

Wasu 'yan sanda uku ne suka shigo da Samora farfajiyar kotu , daya ta riketa ta dama guda ta hagu guda kuwa yana rike ga kulki ta bayanta, a daidai wannan lokaci ne kuwa alkalai uku suka shigo ta kofa mai fuskanta kofar da samora ta shigo , suka daew kujerunsu a cigaba da sauraran kara .

Alkalin yace "kin tada yamutsi...kuma kina shirin jefa atalin jama'a cikin hatsari"

Samora tace " kamar yaya kenan?"
Alkali yace saboda kin sa mata yajin aiki , kuma kin sa su nemi kari albashi , wannan kuwa tattalin kasa bazai iya daukan wannan nauyi ba ,"

Samora tace to mai shari'a tambaya ta anan itace ya akai tattalin kasa ta iya jure yaran da ake miliyoyin yaran da ake tsinta a juji da jikkatan rabin matan faransa amma ya kasa daukan nauyin matan da aka zalunta?

Alkali yace " wannan ba hurumi na bane?"

Samora tace to yakamata ka kama bakinka kayi shiru saboda inda matsalar take kenan, maza suna son mata a matsayin masu hidima da debe kewa ba tare da lura da hakkin da ya rataya akansu ba.




Alkali yace kece mai tada zaune-tsaye da ruguza arzikin kasa da bijirewa da doka da oda''
Samora tace '' ko kadan baka sani ba , manufarmu a baiyane take , '' mace uwa , mace matar aure , ma'aikaciya ba abar muzgunawa ba ku kuma kuna so ta zama karuwa ko tsintacciyako baiwa''

Alkali ya mata tsawa " wa yace miki mata yamutsi suke so "
kawai sai wata mace tai caraf ta cafe maganar tace " mata abunda samora tace suke so , me yasa Mr Andrew ya hana mata sanya ........, harda musu barazana da koransu a aiki?"
me yasa daruruwan mata ke mutuwa a guguwar kankara ?

Sai matar ta dan dakata sannan ta ba kanta amsa tace:
" saboda su tdintattu ne basu san tausayin uwa ko uba ba , sune tsofaffi da mazajensu suka koresu , sune munana wadanda maza basa kula su saboda Allah bai musu kyan fuska ba .... wannan shine adalci?
To idan haka ne adalci , me zai han mata mutuwa a guguwar kankara saboda bata da da mai tausaya mata ko miji mai kare mata kimarta ko gidanda zata amunta a ciki , in kuwa ba haka badole ta fito neman abinci, daga nan ta mutu cikin kankara.

Wannan shishshigi na wannan tsohuwa ya fusata Alkali yace " ke kuma wa ya baki damar yin magana ba ke ba shaida ba ba komi ba"
Tsohowar ita ma tace " ina kare 'yata ne samora , wannan kuma hakkina ne , kuma nima ina kare 'yancin dukkan mata ne"
Koda Samora ta duba sai taga cewa wannan hakika mahaifiyarta ce duniya ta koya mata darasi, komi nata ya fita a haicinsa sai ta fashe da kuka , sauran jagororin kungiyarta suka zo suna rarrashinta.

wannan yanayi ya dauke hankalin 'yan kallo daga Alkali zuwa ga Samora da mahaifiyarsa , don haka ya daga zaman kotu , zuwa mako mai zuwa , yayi umurni da a mayar da Samora kurkuku



- 24 -

Mr. sufan koda abun ya kakare masa sai dauki alkalami ya rubuta makala ya aika ta ga jaridu yana fargar da mutane kan irin kuncin da samora ke nufin jefa mazan faransa , yayi bayanin cewa matukar aka sake ta cimma manufofinta , to da mazaje dakanarin keji baza a banbance wanda zaifi shiga kunci ba.

ita kuwa samora tayi yekuwa a birnin faris tana mai cewa :
" wadanda ke hana maje hakkinta sune masu kokarin saka al'uma halin kakanikayi, sune masu nufin cika faransa da tsintattu da marayu , amma ita mace taushin zuciyarta bai yarda da haka ba, so suke suyi nishadi da mata , su kuwa matan aure suke fata su zama , suna fatan mata suyi aiki dare da rana kamar inji kan albashin da bai taka kara karya ba , wannan kuma zalunci ne da bautar da bazata yarda dashi ba . don haka ku matan faransa inhaka kuke so sai ku burtsar da ra'ayinku .

Nan take sai zanga-zanga ta ta kaure , 'yansan da suka ringa kodawa matan nan kulki , suna fesa musu ruwan zafi , wasu kuwa na jefa musu barkonon tshohuwa.

Amma fa duk wannan bai hana su rera wakokin jinjinawa ga ra'ayoyin samora ba wanda mazajen faransa ke ganin ra'ayin rikau ne.

A tunanin samora da manyan mukarrabanta duk da dukan da sha kamar turmi wasu har sun suma wasu sun raunata amma wannan zanga-zanga tayi nasara saboda sun saka tsoro a zukatan mazaje masu son kansu , sannan sun kara karfafa zukatan mabiyansu sannan sun jawo hankalin hukuma kan al'amarin da da sukewa kallon hadarin kaji.

sai dai a yammacin wannan rana wani bakin hadari ya turnuke sama , akayi ruwa kamar da bakin kwarya da kuma guguwa mai karfi , kowa ya fake a gidansa sai dai matan nan masu sharan tituna , su kan basu kubuta daga wannan bala'i ba.

nan take su samora suka tattara fayil din takardun da suke tattaunawa suka fita don ganewa idonsu labarinda yazo musu . duk wanda ya ga wanda suka fada cikin wannan masifa sai yayi tsammanin anyi ta ne ga tsofaffi ma rasa galihu da munanan budurwai da kuwa kyawawa n da aka tsinta suna yara , duk kokarin wadannan mata shine su kama hannayen junansu kada iska ta musu dibar takardu don a ganinsu sarkin yawa yafi sarkin karfi , amma wannan bai hana daruruwa sun mutu sakamakon daskarewan jini ba .

samora suka jidi wadannan mata zuwa asibiti don samun agajin gaggawa , cikin hanzari har ta ciccibi mahaifiyarta , samora bata gane ta ba , ita kuma ta riga ta suma , koda gari ya waye kungiyar samora sukayi jerin gwanon motoci cike da gawauwakin mata zuwa makabarta, wannan wulakanci da jinsin mace ke fuskanta yasa samora kuka matuka ya kuma dogar da ita kan muradunta


- 25 -





- 26 -


samora ta kasa barci tana karanta littafin RAYUWAR MUHAMMAD tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, saboda a kowane shafi sai tayi kicibis da abun mamaki
Miji shi zai biya sadaki in zaiyi aure!
mazinaci za'a jefe da duwatsu har sai ya mutu!miji shi zai ciyar da gidansa da matarsa da 'ya'yansa!
Aljanna tana karkashin digadigan iyaye mata ne!
Bin iyaye farilla ne!
Iyaye su kula da 'ya'yansu wajibi ne!
kuma wajibi ne namiji ya kula da yar'uwarsa!
Mace tana cin gado kuma tana gado da dukiyarta!
Ba shan hannu da mace muharrama! Ba kataituwa !
Ba zina ! ba kallo!

Tufafin mace zai rufe mata dukkanin jikinta!
Mace daidai take da namiji a hakkoki, sannan hakkin kula da rike gida ya kan na miji ne !
saura kiris ta sa ihu saboda duk kiraye-kirayenta da abunda take mutuwa saboda shi akwai shi cikin addinin Muhammadu Tshira da amincin Allah su tabbata a gareshi irin yadda bata tsammani.. , don haka taba Sonda da Hamonei da dukkan matan kurkukun labari , sai taga sahunsu ya dare biyu, wasu suna kakausan suka Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam , sai ta kame bakinta , amma ta cigaba da karanta dukkan littattafan da dan'uwanta yake kawo mata duk sanda ya kawo mata ziyara kurkuku kan musulunci da manzon Allah Sallallahu alihi wa sallam, da zamansa da matansa , sai taga cewa shine kawai abun koyi wajen kulawa da so da tausayi.
Hakan ne ya sa ta yarda da musulunci , da Muhammad Sallallahu alaihi wa sallam , to amma matsalar itace yaya zata zama musulma? bata sani ba , kuma bata tambayi kowa ba.
Sonda da Hamony ma sun bi tafarkin ta , saidai dukkansu basu gayawa kowa ba.





28



An dawo kotu karo na biyu , mai shari'a sofan ya zauna kar yana kokarin daukan fansa kan cin mutuncin da Samora ta masa , don haka bai barta ta ce komi ba, saikawai yace '' kotu ta yankewa Samora daurin shekara daya cikakkiya , saboda angiza mata su tada yamutshi , da sa su yajin aiki , da dakatar da anfanin jama'a"
Saidai abun bai zo masa yanda yake so ba , don kuwa take matan suka kutsa kurkukun suka , suka kekketa takardun kotun, suka ciro Samora suma ihu:
" Samora ! Samora ! ,
muna son miji ne ba dadiroba !
muna son dan halal ne ba shege ba!
rayuwar mutunci.. ko mutuwa!

Nan take 'yansanda suka bisu suna kokarin tarwatsa su , saidai hakan yaci tura.
Samora
Samora ta hau wani tudu a gefen hanya , mabiyanta suka mata zobe sai ta bude muryarta : zan tafi kurkuku inyi shekara daya , bayan haka kuma zamu hadu , mu ba ma son barna ! hakkin mu muke nema ! kuma gwagwarmayarmu ba zai yiyu ta kare ba sai mun sami hakkokinmu, in kuwa ba haka ba to su kuku da kansu !

mabiyanta suka fashe da kuka suna cewa : saisamora ! sai Samora!

sai ta kara da cewa in harkuna son Samora to kar ku bar hakkinku..

miji ba dadiro ba!
Dan halas ba tshintacce ba!
Uba da uwa da 'yar'uwa da dan'uwa a gidan mutunci!

kuma ina mai kara wa da cewa " ya wajaba miji ya biya sadaki, ajefe mazinaci har lahira .

Mabiyan Samora suka fashe da kuka na bakin ciki da farin ciki tare, wani mutumi da yanayin ya sa masa karsashi yace " nima macen aure da dan halal nake nema ! ina tare daku! zan daukeku aiki a masakata da albashi irin na maza kuma baza ku wuce sa'a takwas ba!

wani kuma yace " ni dan majalisane zan kawo ra'ayin amincewa da bukatunku "

kafun ya kare bayaninsa sai yan sanda suka yi awun gaba da ita sai jami'a annabi yusufa ALAIHISSALAM






- 29 -


Majalisa ta dau tsawon wata shabiyu ta tattauna ra'ayin dan majalisa moleh , a birnin Paris kowa yana bibiyan labarin tattaunawa, kullun kuma cincirindon mata ne ke makire majalisa
da zangazangar lumana kan tituna , samora kuma tana turo musu sakonnin karfafa guiwa daga dakinta na kurkuku, har saida shekara ta cika.

Dubannain mata sun hadu a kofar jami'ar Annabi yusufa Alaihissalam, suka yi zuga suka kaita gidansu , hakan yasa { jabon} kukan farin ciki don fitowar Sonda , shima {borjeih} ya gamu da masoyiyarsa { hamony} ya nemeta da aure , sai tace masa : " nawa zaka biya sadaki? " yace mata " duk abunda kike so ''

sai tace '' zamu hadu gobe mu tattauna''.


Ba zata samora tana shiga gidanta si taga babanta yana kuka, duk da cewa tsufa amma yayi matukar farin ciki da ita matuka , can tsakiyar dare sai suka ji ana kwankasa kofa , {hamony} tace ba shakka {borjhei} ne '' ashe snith mahaifiyarta itace a kofa , samora tayi tsalle ta rungumeta : '' mama! mama! '' sai suka fashe da kuka shima tsohon ya sa kuka don murna , ya tashi ya mika mata hannu suka gaisa sai tace '' zaka in dawo maka uwargida mai ladabi? , sai ya kara fashewa da kuka don farinciki da tausayi .
sai aka kara kwankwasa kofa , {borjhie} ya shigo , yace nazo neman aure ne da {hamony} , sai Samora tace '' bayan ka zama musulmi mai ladabi wa mahaifanka kenan , don [hamony } musulmace , bazata auri wanda ba musulmi ba''

suka shude wannan dare cikin tafka muhawarar da karshenta {snith} da {borjhie} da {bytan} suka musulunta , {hamony } tayi aure , wannan dare shine dare mai dadi ga Samora.

koda ta sami labari sai ta sanya kayan maza ta buya, titunan faransa sukayi makil da zanza zanga da bore ga masu muzgunawa mata , masu sonta a matsayin farka ba matar aure ba, masu samar da tsintattu da marayu ba 'ya'ya da suka sami tausayi uwa da uba ba.

Matakin da majalisa ta dauka bayan doguwar muhawara shine suyi kafar angulu ra'ayin { molieh} , sai ma suka ciro dokar hana mace yajin aiki , suka goge mata duk wani hakkin gwagarmayar siyasa , da kin duk wani sauyi kan yanayin da suka sanya mace a ciki na tsawon shekara biyar ala-akalla.

'Yan sanda sun yi zobe wa gidan Samora , ashe ma bata ciki, tana gidan wanta {borjhie}..

Hakika faransa ta kadu matuka lokacin da yansanda suka sanar da kisan , mata kuma suka tada bore mai zafi don 'yanta mata , saidai abun tambayar da ke jefo kanta itace : '' shin wannan bore zai yi nasara bayan kisan samora???? ''


Ba shakka ya zama dole juyijuya halin mata ya yayi nasara a dukkan duniya, dole su tabbatar da abunda Allau ya basu, dole su dawo kamar yadda musulunci ya ke so su kasance ... masu daukaka ... yantattu.... matan aure ba farkoki ba , uwaye ba masu baiwowi ba , karramammu ba wulakantattuba, to yaushe hakan zai yiyu?

Yaushe mafarkinsu zai zama hakika .

Ba sai jakin baba yai kaho ba don komi tsayin gari zai waye.

Ba shakka gari zai wayewa matan faransa

9.8.08

Rayuwar da Alkalami bazai manta ba


Ya salam ! , komi yai farko zaiyi karshe , shekara kuma kwana ne , kamar kwana hudu da suka gabata na sauka a filin jirgin Khartoum da Abokan karatuna kamar karfe 9:00 pm , lokacinda aka fito damu zuwa masaukinmu ba abunda nake kokari sai in kalli yanayin farkon kasar da na fara shiga ba tare da na kyafta ido ba , musamman sanda muka hau gadar da ke kan Nilu in da na hangi wani dan karamin tsibiri a ciki , haka dai cikin kallace-kallacen gari da masu garin , muka isa masaukinmu , wasu fuskokinda dama munsansu suka taryemu da sowa , wadanda suka fara ganinmu a ranar kuma suka mana barka da zuwa kowa yaje kashe wutar gabansa .
Ni dai fatata da tsikar jikina tana isar mun da sakon bakunta , da kewar gida Najeriya .

Wani gari da waye , dan uwa Bashir ya tattaremu muka je wani abu mai kamada rangadi a Jami’ar musulunci ta Omdurman (Omdurman Islamic University ) wacca itace aka bamu gurbin karatu a ciki , dama dai ina da karamin sani dan gane da Jami’ar , saboda kanen kakana Ambasada Abba Abdulkadir samada shekara 30 shima nan yayi karatu , wata ran kuwa da akayi sharan dakin littafansa , an bani wasu littafansa daga ciki harda Dalilin( brochure) tsangayar osuluddin , a matsayina na dalibin Arabiya .

Mun fara karatun A jamiar inda na shiga tsangayar shari’a and law , muna tattaki wani lokacin yayi saibi kamar tafiyar hawainiya wani kuwa muga kyaftawa da bisimillah ya gilma kamar walkiya , wata rayuwar tai mini zaki kamar zuma wata tai mun daci kamar shuwaka , wata kuwa tamun tsami kamar tsamiya , tsada ko lemon tsami .
Mun shiga fargaba daban daban kamar mutuwan mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan tawaye daya fadi a jirgi bayan kwana Ashirin da bashi mataimakin shugaban kasa , cikin birnin Khartoum ya dauki dumi don kuwa wasu sun rasa rayukansu wasu sun rasa dukiyoyinsu wasu matan kuwa sun rasa mutuncinsu sakamakon fyade da mutanen mamacin sukayi da hujjar cewa hukuma ce tai kutunguilar kashe shi , ni dai ban rasa komi ba sai aminci da tsoro ya koreshi , sai kuma hawaye saboda wata motar kabokabo da aka kona a kofar gidanmu , hayakinta ya ringa tultula gidanmu .

Abunda yafi tada hankalina babu kamar rashin lafiya da nayi a karshen shekara ta uku wata biyu ana mun allura ina kuma hadiyar kwayoyi takwas, sauran wata shida kuma ina shan kwayoyi bibiyu duk wayewar gari . wannan mawuyacin yanayi da jikina ya shiga ya kama hanun zuciyata sun tafi don kuwa har nayi shawarar jingine karatun zuwa shekara mai zuwa in dawo gida don jinya ,
Cikin wannan rashin lafiyar kuwa Allah ya jarrabeni da yan sudan don kuwa farko-farkon ciwon wataran na kama hanya zuwa asibiti ina tattaki ina karatu wani sa’in ina wata yar waka da zata sanyaya mun zuciya ita kuma ta sanyaya mun jikina , ni kuwa kaftani nasa ba jallabiya ba, ba kuma hula kaina, hankalin suma ta ya tashi, ban tsammanin za'a rasa gashin bargo da suka kulla abota da gashina wanda da a kasar hausa ne da yara sun min wasan '"ga wani a bu a kan matan sarki" . ban karkare tone tonen tunani na ba sai sai naji tsawa a baya na

" kai ne limamin wancan masallacin ?"

sai na farga a firgice naga wani mutum a yankwane, kasusuwa sun baiyana a fuskarsa , gajere , idanunsa sun yi jajazur kamar gauta , gashi ya daka mun harara. Ya kuma nuna wani masallaci , wanda ni banda wata alakata dashi data wuce cewa wani lokaci na kanzo karatu ciki ba , anan ne kuwa na taba ganin tsohon shuguba Sadiq al-Mahdi yazo daurin aure .

" a'a ni ba liman bane " nace

" to kai me ye? " ya ja gurrnani kamar zakin da aka tsokana

sai naga abun sai hauhawa yake , ga shi sai kokarin huruwa yake

" ni dalibin jami'a ne " nace masa

sai ya zaburo kai na yana nuna mun kashedi yana cewa " wai shin ku 'yan najeriyan nan kafun kozo sudan ba musulunci ne ko yaya?

na shafa ko zan ji hakurina , ashe ya sace mun , don haka nima na haukace na fara maganganu da ba nutsuwa ciki " ina ruwanka da 'yan najeriya " " me suka ci maka basu biya ba " .


Kafin in kare zaiyano abunda ke kwakwalwata sai kawai naga ya suri hoge mai girma wai zai mun rotse
sai nai shiru ina kada kai , na laluba kamus din kaina ban sami komai ba sai wasu kalmomi sai nai maza na hadasu nace " ZA-KA-MUTU! "
Ko da yaji haka sai yace " ka kashe ni a kasa ta? , wannan kasar muce mu mukai gwagwarmaya akan ta "
ba shakka ya fesa mun tsoro a zuciya ta, kuma yasa nayi bitar jimlar da na hada , na karanci ma'anar ta a take sai na fahimci cewa ma'anar ta shine in kashe mutum a garinsu " dukda cewa dai dama barazana ce ,sai nayi wasu yan sunbatu ina ja da baya da yan dabaru , har na samu na gota shi kuma ya haye katangar hubbaren wani shehunsu mai suna HAMDANNIEL kamar kadangare da dutsen a hanunsa, ni kuwa na wuce ina yiwa kaina barka a raina , don kuwa da ba don kariyar Allah ba da ya kara mun kwankwatsar kayi kan zazzabin nan.

To amma abun tambaya shine me yasa wannan mutumi ya shiga rayuwata na 'yan wadannan dakikai?

AMSA shi dai wannan bakauyen yayi tsammanin cewa najeriya duk kiristoci ne saboda yaga shugabanta Obasanjo kirista ne kuma dimukoradiya ta kawo shi , sannan galibin yan kwallon najeriya yaga ba sunan musulmai gare su ba, har sun yi tsammanin Jay Jay okocha musulmi ne mune bamu iya fadan yadda sunan yake a larabci ba wato UKASHA, to duk da haka sai yaje yin salla wami masallaci sai ya tarar limamin dalibine dan Najeriya , don haka yake ganin bai dace ace wadanda suka musulunta jiya da daddare sunzo suna limancin wadanda suka gaji musulunci kaka da kakanu ba.

Amma kai meye ra'yinka

sai naji daga gareka
Bayan kwana biyu ko kasa da haka ko sama da haka wani abunda da yafi takaici gareni ya faru , shima na fito zani Asibiti ban san sami mota da wuri ba , sai daga karshe motar da na samu ta cika sai a tsaye na tsaya banyi auni ba sai naji naushi koda na juyo sai kowa yak au da kai , sai kawai wani baba dake bani hakuri , koda na kuma juya wa sai na kuma ji wani naushin sabo , na juyo cikin fushi da radadin rashin lafiya , sai babannan ya kara bani hakuri , duk wadannan naushe-naushe ban san mai yinsu ba kuma ban san daliliba , sai daga karshe naji wai sanda nake tsaye na taka wani dan kudancin garin kuma da alama cikin maye yake , amma abun mamaki koda nayi martani cikin fushi sai na zama mai laifi , mata da maza na mota sukace dama mu baki mune muke kawo rigingimu cikin sudan , muryoyi daban daban wata a baiyane wata a dashe kowa yana mun tofin Alatsine , koda naga abun ya kasa hawa mizanin adalci saina dakatarda Karen mota nace ya sauke ni na kara da addu’a a baiyane kowa a motar saida yaji nace “ Allah ka fitar damu daga garin azzalumai ” .

Wadannan ababa da suka faru dani har suka sani cikin damuwa wani abune dake gwada cewa rayuwa launin fari ne wata ran kuma baki wataran kasha zuma ,wataran kuwa kasha madi , wataran kasha madaci ,don kuwa zaiyi wuya mutum ya sami mutumin kirki a doron kasa kamar dan sudan mai girmama kowa da rashin girman kai , mutane duka daya ne maikudi da talaka , koda kuwa shugaban kasa ne , yana daga abunda muka ji labari daga wadanda suka rigayemu cewa sanda akai wuyar man fetur a kasar shugaban kasa in ya fito yakan debi yan kasa ya rage musu hanya , lokacin muna nan kuwa wataran da sudais ya kawo ziyara kasar jama’a kamar tawagar tururuwai kowa na so ya gaisa dashi , koda shugaba yaga an gajiyar da bakonsa sai ya kutso ya tare shi yaba jama’a baya yana hanasu sai suka ture shugaban kasa yai kasa koda yaga abun yafi karfinsa saiya ja gefe , muma almajirai mukan halarci wasu tarukan da shugaban kasa ke zuwa kuma mu zauna a sahun gaba – gaba , ina tuna wata ran da ya shigo taro aka mike ana taken kasa nidai da Habib tijjani da Ibrahim muktar bamu mike ba kuma tsakaninmu da shugabansa baifi sahu hudu mukai ido hudu dashi amma muka ki mike , kuma muka ki mike wa muma mu sandare , Allah ja zamaninka Bashir .

Cikin wannan tattaki daga yini zuwa yini ,mako zuwa mako , wata zuwa wata , shekara zuwa shekara , muka farka muke jin kamar labarin cewa muna shirin jarrabawar fita a jami’a , wannan ya razana zuciyata matuka , musamman inya tuna cewa ya kamata mutun ya karbi sakamakonsa da hanun dama yaje gida yana kadata kamar tuta kowa ya gani , muna cikin jarrabawa “ wataran ina karatun jarrabawa a wani masallaci mai jan fenti a gefen titi , dama dai munji wani abukamar jitajita cewa yan tawaye zasu shigo da niyar juyin mulki , amma duk mun dauka kamar yadda suka saba ne , suce zasu zo amma ba ganin ko kuransa , da haka nidai na dauko littafin Public finance ina karantawa saboda jarabawansa zamuyi jibi , koda na leko ta taga sai naga gare ya sake fuska kamar ba wanda na sani ba sai na fito in ganewa idona koda muka fito sai naga jerin gwanon motocin masu sulke da na take suka fara bude wuta cikin iska , wani yanayi ne wanda ban taba tsammanin zan sami kaina a ciki , a lokacin na san ma’anar tawaye da kokarin juyin mulki , ana ta rowan harsashai masallaci kuma ya zama kamar kasuwa kowa ya fado ciki , maza da mata , musulmi da aljihun baya, kowa wasu na rarrafe wasu na ni kuma ina bayan ginshikin masallaci tsoron kada a harbo wani abu ya fasa gini ya shigo ya mun rauni , kuma ba shakka hakan ta faru amma Allah ya tsare , sudai wadannan yantawaye sun fara jin kanshin gidan shugaban kasa , amma karshe sunyi kicibis da dakarun hukama inda aka ba hammata iska aka taushe su aka kamasu , sai dai abun takaici cikinsu akwai kananun yara yan shekara12 , 13, 14, wasu an kaisu barzahu wasu an kamesu .

Cikin bugawar zukata muka kare wannan jarrabawa amma da ikon Allah sakamakon ya fito na sami matakin na biyu a tsarin darajar sakamako wato Very good wanda yake farawa daga 70 zuwa 79 ,

Na kare rayuwata ta sudan zan barta ina mai tuna ranarta da tasha banban da irin ranar sauran duniya , wacca Allah ya kwararar da Nilu a cikinta manoma suna kwararawa wa gonakinsu dake bakin gaba , makiyaya suna shayarda dabbobinsu , masunta suna kamun kifi , ni kuwa almajiri a ina shan wata iska mai debo danshi zuwa gare ne , ina jin dadin haddan abun day a wajaba in haddace , ina fahimtar abunda ya wajaba in fahimta , ba shakka rayuwa ce mai dadi amma ban san abunda yafi dadi ba shin sanin wani waishi bashir dab sakkwato , wanda ya dauke ni kaninsa yake ban hakuri don inci abinci kamar karamin yaro , wanda ya gama karatunsa ya tafi ya barni kamar maraya , ko haduwa da Mustapha bangon gishiri dan shehu barnoma , ko Habibu tijani da muka karasa rayuwar da muka fara a Jos ko Ibarahim dan baba wanda na sanshi a nan sudan amma kamar tare mukai yaranta , ko yusuf Nabahani comtuper man , ko Awwal bakoshi bangon dutse mai wuyar isa , ko umar hamza maim un ahnun ka mai sanda daga nesa , ba shakka rayuwace mai zaki kuma wucewarta daci ne dauwamamme .

Bazan iya mance kirkin muttanen dakin da nake kaikawo zuwa gareshi ba , sai sani musa ya miko mun magani na in sha , kabiru a bamu wani labarin raha , Naziru ya fadakar dani zubairu miko mun taliyar Indomie , bana fita daga dakin sai sun warkar da jikina da zuciyata , Allah ya bar zumunci.

shin zamu iya fahimtar gaskiya tsakanin shi'a da sunna ta waki'oin siyasa ?

Iran da Amurka fuska biyu ga kobo daya

Dalilin wannan tambaya shine wani rubutu da naga wani bawan Allah yayi yana mai tabbatar da ingancin mazhaban shi’a wanda ya ginu kan zagin sahabbai , da matan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi , da irin gaban dake tsakanin Jamhuriyar Iran , da kasar Amurka , ko artabun da akai tsakanin Hizbullah da Isra’ila .

Sau da dama hakan ake tunani , sai muyi wa mangoro hakunci da bawon da ya lillubeshi , wannan kuwa zai boye mana da dama daga cikin gaskiyar da muke nema , wannan ma ya tunamun wani da yayi shigan wani Akaramakallahu , da babban rawani da duk kayan da jama’a zasu yi tsammanin Shi na kwarai ne , ya sauka wani gida wanda daga karshe ya sace musu yaro yayi gaba .

Ya kamata mu tuna cewa siyasa abace da ke ta’allake da alfanu , kowace kasa ta hangoshi zata garzaya ta kawo wa kanta , ko da daga makiyarta ce , sai tayi mata zakin baki da lallashi , don haka wasu suke ganin siyasa ba makiyi na dindindin ba kuma aboki na dindindin .

Ita dai gaskiya daya ce amma in muka dauki ma’aunin da wannan dan shi’a ke amfani dashi zamu ga gaskiya sun zama barkatai , saboda Amurka bata da abokin gabanda ya wuce Osama ben laden , tunda shine ya kwance mata a kasuwa , ya gwada wa duniya cewa Amurka bata isa tayi aikin Allah Ta’ala ba . kuma har tayi nasarar tabbatar wa Al’umar duniya , majalisar dinkin duniya da daukacin kasashe cewa shi dan ta’adda ne kuma ya wajaba a kawo shi ko gawarsa , alhali kuwa bai taba hada hanya ma da shi’a ba bare ya shiga .

Akwai misalai da dama da zai tabbatar mana da cewa siyasa babu wani hali mai dorewa wanda ba mamaki babbansu ya zama alakar Iran da Amurka ta inda suka raba gari wajen mas’alar makamin kare dangi , sannnan sukayi taraiya wajen kawo tashin hankali , da kawo rudu a kasar Iraki, musamman in muka san cewa Badr corps da jaishul mahdy a iran ake horasu a turosu don zubar da jini da tarwatsa garuruwan Ahlussunnah , duk su gudu don kar ya zama suna da wani matsuguni na musamman , don Shi’a su zama sune mafi yawa .

Yayin da muka so sanin zurfin Alaka tsakanin Amurka da Iran wanda masu sharhin siyasa ke ganin fuska biyu ne ga kobo daya , tana nan tun baiyanar Khomeini a matsayin dan hamaiya ga hukumar Shah . cikin Hirar da akayi da Bani Sadr (shugaban kasa na farko bayan juyin khomeini) a shirin ZIYARA KHASAH a gidan talabijin na Aljazeerah ya tabbatar cewa “ wakilan White House sunzo don ganawa da Khomeini a Neauphle le chateau inda yake gudun hijira , wanda Ibrahim Yazdi ne ya taryosu (wazirin harkokin waje a hukumar Mehdi Bazargan ) , anyi zaman da ya hada da jakadan Amurka a Tehran da Mehdi Bazargan da sauran ayoyi wanda suka dauki matakin hadin guiwa tsakanin malamai da sojoji don a samar da tsarin siyasa tsayaiye a Tehran ”, haka kuwa Khomeini ya bar Paris cikin jirgi mallakar faransa wanda aka ware masa shi da masu dafa masa baya ya sauka filin jirgin Mehrabad na Tehran 1/2/1979 abun mamaki Amurka bata tanka ba .

Zaiyi wuya wani ya gaskata cewa ba hanun Amurka a kifar da mulkin Shah saboda a daidai lokacin da hakan ya faru akwai sojojin Amurka 40,000 dubu arba’in suna aiki ma’aikatar jikin gida da tsaro da SAVAK ( Hukumar liken asiri ta a mulkin Shah ), kuma suna da tare da manyan kayan liken asiri.


Har wayau dangane da kawancen Iran da isra'ila Bani sadr cewa yayi
“ lokacinda mukai zama da sojoji ,wazirin tsaro yai bayanin cewa abun muke shiri shine sayan makamai daga Isra’ila , munyi mamakin hakan , don haka na tambayeshi , waya saka hakan? Yace : Imam Khomeini , nace wannan bazai yiyu ba , yace kasan bazan yi hakan da radin kaina ba , don haka na garzaya don ganawa da Khomeini na tambayeshi , kai ka bada dammar haka ? yace eh musulunci ma ya bada dammar yin hakan , kuma yaki shine yaki, abun ya daure mun kai , ba shakka haka ne amma ni nayi tsammanin yakinmu tsabtatacce ne , kuma jihadi shine mu yardar da yan’uwanmu su dakatar da yaki su fuskanci zaman lafiya , wannan abunda da ya wajaba ba zuwa sayo makami a Isra’ila don yakin larabawa ba, bazan yarda da haka ba , sai yace mun “ kai kana adawa da yaki , kuma dole ka yi don kaine a gurbin jagoranci ” haka babban wazirin Isra’ila Menachem Begin ya tabbatar da cewa suna taimakawa kasar Iran da makamai , shi kuma Ariel Sharon (wazirin tsaro a wancan lokacin) ya baiyana cewa suna hakan ne don raunana Iraki .

Daga cikin abunda ke razana Iran babu kamar wata kasa ta zanto tana makwabtaka da ita kuma jagororinta daliban addini ne wadanda basu bata kwakwalensu da munafunce-munafuncen siyasa ba , don wannan zai hana shigarda shi’anci a duniya , don haka ba wanda yaci moriyar ranar 11/9/2001 kamar Iran , don haka faduwar hukumar Taliban tamkar sakiya ne ga marurunta , kuwa tun tuni tana taimakawa Northern Alliance dake Mazār-e Sharīf , da tsirarun yan shi’ar kasar dake yankin Bāmiān har takai ta fara barazanar kawo sojojinta a iyakarta da Afganistan to kada Amurka kudiri aniyar yakar Taliban sai zamu ta tarda mujemu . don haka Iran ta hanzarta yarda da hukumar Hamid Karzai wanda Amurka ta kafa , shi yasa jakadan Iran a Afghanistan Muhammad Ridha Hashimy yace “ sabanin da ke tsakanin muda Al’ummar duniya tasirinsa bai baiyana a Afghanistan ba har yanzu ,kuma muna ganin lallai Afghanistan zata iya kasancewa sanfuri ga irin taimakekeniya tsakanin Tehran da Al’umar duniya ” kuma kowa zai iya fahimtar ma’anar Alummar duniya anan da cewa Amurka ake nufi , don sune jagoran yaki .

Har wayau Muhammad Abtahy a taron da sukai a Abu Dhabi
“ da badon Iran ba da Kabul da Bagadaza basu fadi ba ” .

Taraiyar Iran da Amurka kan yakar Iraki a 2003
Iran ta yi ruwa tayi tsaki wajen wannan yakin kai tsaye ko sunkuye ta hanyar Da‘wa Party da Supreme Council of the Islamic Revolution in Iraq (SCIRI), shiyasa yake a baiyane Amurka ta hada kai da shi’ar Iraki ta kuma gadar musu da mulkin Iraki su kuma sunci karensu ba babbaka kan yan sunna , suka tilasta musu kaura , sun kashe malaman masu adawa da siyasar Iran a Iraki.

Idan mai rubutu zai yi batun alakar hadin kan Amurka da Iran a Iraki (raunanniya) dole sai ya ambato wasu abubuwa kamar haka :

1- Tehran da Washinton suna da wasu cinikaiya irin tasu a boye duk da cece-kucen da suke a kafafen watsa labarai .

2- Ba kunya ba tsoron Allah Iran tayi kakagida kan al’amuran cikin gida a Iraki , don kuwa galibin masu madafan iko kasar imma yan kasar iran ne ko masu Nationality na Iran , sannan Badr Corps da Supreme Council of the Islamic Revolution in Iraq (SCIRI) suna samun horo ne daga Iran sai a watsosu Iraki don kisan gilla wannan duk Amurka tana sane da hakan , amma saboda cinikaiyarsu bata ce uffan .

Har ila yau rahoton da Robert Gates da Zbigniew Brzezinski sukayi kan Alakar kasashen biyu wanda suka samai taken Iran: Time for a New Approach , rahoton ya baiyana mahimmncin ganawa tsakanin biyu saboda dalilan siyasa da istiratijiya na alfanu ga ita Amurkan . haka rahoton da Iraq Study Group da aka fi sani da hamilton / baker shima ya ja kunnen Amurka da ta riki Iran hanu bibbiyu in har tana son kafuwa a Iraki.

Akwai dalilai masu dunbin yawa dake tabbatar da shakikancin Amurka da Iran , kuma wannan su saba kamar yadda harshe da hakori ke sabawa , ko kamar yadda Amurka da Isra’ila ake kai ruwa rana wani lokacin , ko kuma Birtaniya .

Ko kadan banyi wannan rubutun don wanke wani dan siyasa ko wata kasa daga alaka da Amurka ko Isra’ila ba , koda kuwa ta zama kasar sunnah , don kuwa kowace kasa tana da alakokinta da wadannan kasashe biyu saidai wata tafi wata , innama nufina in gwadawa wadannan masu cika bakin cewa Kasar Iran ma’asumiya ce ga abokantaka da yahudu da Nasara , in sun sani amma suke boyewa suyi adalci su fadi gaskiya, in kuwa ana yaudaransu ne to ya kamata su ringa neman sani kan abu buwanda ke gudana .

Mudai agunmu masu neman dacewa da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi , ba’a umurcemu da bin Sa’udiya ba , don haka in tayi wani katobara , baya cikin adalci ace sai mun sama mata mafita ko mu wanketa da karya da gaskiya , Don haka abunda zai daddale gaskiya tsakanin shi’a da sunnah ba abunda sarki Abdullahi ko Husni Mubarak ko kuma a daya bangaren Ahmadi Najad ko Hasan Nasrallah suka yiba , innama abunyi shine a tambatayi ko wani dan shi’a meye matsayin Sahabban Manzo tsira da amincin Allah su tabbata masa agunka , ko A’isha uwar muminai , shin meye matsayin makashin sayyidina Umar mai raba karya da gaskiya, shin abun aje Hubbarensa ne ana neman tabarruki ? . shin Abuhuraira wanda ya kiyaye hadisan manzon Allah tsira da aminci ya tabbata masa makaryaci ne kwadayaiye ? , shin da gaske wai cewa a akidarku in Sha-sauraronku yazo sai ya tashi Saiyidai Abubakar da Umar ya azabtar dasu ?.

Sannan a waiwayi Ahlussunnah a tambayesu shin Akidar ta tanadi wata darajawa da kimatawa ga Sayyidina Aliyu wanda manzon Allah ya shaida cewa yana son Allah , kuma Allah yana sonsa ? , ko Hasan da Husaine wadanda manzon Allah yace sune shugannin samarukan aljanna ? .

Naku Alkalami.

17.7.08

10.7.08

LABARIN MAI JAYAIYA



Wata rana wani mutum mai yawan gardama kan al'amuran addini ya riski imamu Shafi'i , sai ya tambaye shi cikin ba'a " ya ya Allah zaice ya Halicci IBLIS da wuta kuma ace an azabtarda shi da wuta , kuma yaji radadin wutar " sai malam SHAFI'I yayi shiru na dan wani lokaci , sai ya je ya zo da bushashshen laka yazo ya jefi wannan mai jayaiyan , koda yaji zafin wannan lakan yayi fushi , sai malam shafi'i yace " ya zaka ji zafin laka bayan kaima da laka aka yika " sai mutum ya tashi ya wuce kunya ta rufeshi.




1.7.08

لـكِ يا (نمـا) كل الـمودة طـالما
إليك الأسـود الزنج من أرضنا انتـمى
ومـا أنـا لـلأيـام إلا مصـارع
وإن أحـد يغلـبْ فـآخـر يهـزما
فما لـك يـا أيـام تنهين عهـدنا
وعهـد لم ينهـب ولم يـك معـدما
وإن كنـت في صمت فذاك تكلـف
فلـم يك أهـل البر في الحق صـوّما
فأشبعتـها ضربـا بأصـرم من فمي
تنـحّي بعيـدا أو عـليـك التقـدما
فلسـنا نبـالي حين يذهب روحـنا
ويتـرك للبـاقـين مـكـرمــة نما
سمو بك يا هذي الريـاض التي علت
علا قمم واستمطرت من نـدى السما
لـها من ليـال ليـلـة أدبـيـة
تمــد لنـا البــدر المنـير وأنجما
فمـا كنت تحت الضوء حتى أخالني
على درجـات الشعـر أهـوى الترنما
فلا النثـر يحلو دون سجع حروفـها
وما الشعـر إلا من أنـان السـما سما
وإن كـان شـعري في أواخر عمره
وفي آخـر الأنفـاس يتـلوك يـا نما
جـزى الله كـل القائمـين نعيـمه
وكـلا من الأخيـار مـن زار فانتمى
وليـد ومـا بعـد الولـيد وقبـله
أبـو عـاصم والمقـطري الـذي سما
وأيمن ذا صـبر وبكـري ذا تـقى
وعمـار فـي الضـراء واليسـر أفهما
وكنت فدى شيـخ الأمـين وبعـده
عشيـش وفخـر الـدين أمسى معلما
فهـذا لقــرآن وهـذا لـسنـة
وذاك لفهـم الـسـالفـين متـرجما
فلا أبراهام الخـير في الجـد هـازل
ولا جعـفر ينـسى الجمـال المحـكّما
أولئـك أقـوام عـلي لـهم يـد
تمـنّ فلـم تمسـك عـطاء مـكرّما
أيـا نجمـة ودعتـها فوجـدتـني
أسـير أسـيرا فـي الـدجيـة مرغما
وكـان حشـى قومي بحزنيِ مضـمرٌ
وعيـني بـالـدمـع المسـيل مـتيما
ألا ليـت هذي الدار يبقى سـرورها
فأضـحك فـي كـل الزمان وأبسما
ولـكنـه طبـع الحيـاة مـريـرة
لحـينٍ، وذاك الحـين لـيس بـأدوما
فقـد بـان مني الصـالحون عهدتهم
كـأن لسـانـي ذاق مـرا معـلقما
ومـا كنـت أنـسى أن للبين ليـله
ومـا كنـت أدري لـلـمــلاقاة مـوسما
وإن لقـائي بالأحـبة سـلسـبيــ
ل عيـشي فسـلْ عـني السبيل مقيما
أيا جعـفر هـلا بكيت ابن يوسـف
وخــير زمـيل في الحـياة معـظما
إذا ما بكى عبد الكريم ابن حـامـد
فأجهـش عبـد النـاصـر الـمتقدما
وودعــت آدم والفـؤاد و(أولا)
كـذاك حسـينا واحمـديـن يليهما
نذير وجبريـل ونصـر وحيــدر
وعبـد المجيـد والمجـاهـد أكـرما
ولم أنـسى عبـد الله ثم (أبات) مع
سليمان مع (لـولى) الـذي لن يذمما
محمد الشادي و(عبد) و(مـودبـو)
و(كلمي) وعبـد القـادر المتـصرما
فلا (واجـو) ينأى عن سبيل سلكته
ولا ناصـر يـأبى (مهـامـا) المقدما
ثـلاثـون شبـلا لا أبـالك ليتني
أضـاف إليـهم منـحـة وتكـرما
وكيف يكون العيش من دون هـؤلا
فقـد كنت لحما منهـموا ولـهم دما
كظهر لميـع لـو تـعرض قـاطف
لـه بـعد حـين طيـبه لـم يـعمما
وإني لأجـزم أن أبـيض لـو سهى
يـذكرْه نـيل أزرق الـلـون أنجما
تضيئ سواد الليل في القـارة الـتي
علـيها النجـاشي حـل عقدا وأبرما
وفيهـا ابـن فودي إن ترأس جيشه
تسـير الفيـالـق والعـرمرم مـغنما
وكـان العـوالي والأسـنة والـقنا
بـأرض امـدرمـان شـعارا ومعلما
فكيف يكون الـدين دين غـرابـة
فهيا لـها يـا مـن بـأرض نمـا نمى

8.6.08

Ya zamuyi turai su somu?



Shugaban kasar faransa ya jaddada kinsa kan bawa kasar turkiya mambanci a kungiyar taraiyar turai , saboda kasancewarta kasar musulunci.

A da can shugaba Sarkozy yana fakewa ne da cewa turkiya ta sabawa kasashen turai a al'adu da kuma jogiranfance , don haka ba dama ta samu shiga taraiyar turai saboda kar a ringa samun karo , Amma hira da 'yan jarida sukai da shi a ziyarar da yakai kasar Poland ya fito sarari ya baiyana cewa bazai iya yarda da kasar da mafiyawancinta musulmai ne su samu kujera a taraiyar turai ba , koda kuwa sunbi tsarin Ba'addini (sercularism) .

Wannan bayani zai iya baiyana irin kiyaiya da Sarkozy da sauran kasashen turai suke wa islama da kuma fargabar yaduwansa a cikin al'umarsu , sannan hakan ya kaisu ga kokarin kashe musulmai don kokarin rage adadinsu a duniya musammam in muka dubi karfin soji da Amurka ke kashe Iraki da Afgahnistan dashi , da durawa wa yara 500 kwayoyin cutar Aids a kasar libiya da majinyatar kasar Bulgeriya sukayi wanda shi Sarkozy da matarsa da ya rabu da ita Cicilia sarkozy sukayi ta fadi tashi saida shugabn Libiya ya sake su da sharadin za'a hukuntasu da dokokin kasarsu , amma koda suka sauka a filin jirgin kasarsu sai hukumar kasarsu ta sanar da cewa ta musu afuwa .


Idan muka waiwayi tarihi zamu fahimci cewa birnin Istanbul ko kusdandiniya (constantinople) shine ya mulki duniyar musulunci bayan daular Umawiya da daular Abbasiya tun 1290 karni na 13 miladiya har zuwa 1923 sanda Mustapha kamal Ataturk yai kutunguilar rusheta .

Wannan kangararren mutumin ya shahara wajen kin musulunci da kawazucin al'adun turai , har an rawaito yana cewa " ya wajaba mu tattari daukacin Al'adun turawa kyawawansu da munanansu harda tsutsotsin tumbunansa" don haka ya hana kiran salla da yaren larabci , ya kuma hana gaisuwa da lafazin " Assalamu Alaikum " saidai a sha hanu a wuce , sannan ya haramta auren sama da mace daya , da sanya hijabi , ya musanya kalandar Hijiriya da ta miladiya, ya musanya hutun mako zuwa lahadi maimakon juma'a , sannan ya musanya dokokin shariar musulunci da daular usumaniya ta ke bi da dokokin kasar Switzerland (Swiss civil law) 1926 , duk don ya samu karbuwa ga turawa , da alama bai taba karanta ko jin fadin Allah ta'ala " yahudu da Nasara baza su yarda dakai ba sai ka bi tafarkinsu " kamar yanda Suhgaba Sarkozy ya tabbatar da hakan.


Naku Alkalami

4.6.08

Malam Isa da Alhaji Mu'azu



Ba shakka tunda aka fito da wannan sabuwar siyasa ko ince tun 1999 Malam isa yuguda ne yayi gwamna a jihar Bauci da zabe mai tsarki , don kuwa zaben farko tsakani PDP da APP ba Ahmad Mu'azu ne ya lashe ba , baba Ajiya ne yayi kaye ( kan wuka mai wuyan kamu) amma tsagera suka masa rashin kunya , sannan lokacin ta zarce ma baici ba saboda kowa na bukatar masara ida a rufe don haka masara sak ! ake yi . Amma da tura ta kai bango lokacinda jama'a suka fahimci cewa wannan mu'azun dan rainin wayo ne , suka fito kwansu da kwarkwatansu don su hana shi sanata su hana dan gaban goshinsa Nadada umar gwamna , suka sadaukar da kansu suka don kwato yancinsu daga mahandama , suka tabbadar hikimar Hausawa mai cewa " Sarkin yawa yafi sarkin karfi " .
sau da dama yayin da za'a zalunci mutanen bauci , da sunyi wani dan kokarin kwato hakkinsu sai wani mai anguwa ko yaje gidan rediyo yace wai an san Bauci da zaman lafiya , tun sanda Shehu usumanu ya musu addu'a " . ko me yasa jama'ar Bauci suka yasar da irin wadannan sakarkaru maganganu? , ina ganin wuce irin azaba suka sha a zamanin Amadu mu'azu.
A zamanin Amadu a tunanina babu wani abun da yayi wanda ya ja hankalina kuma na jinjina masa kamar kokarin da yayi na taimakawa musulman pilato , fara daga rigimar addini na 11 ga watan satumban 2001 har izuwa rikicin yalwan shendam , ba shakka wannan abun azo a gani ne.

Wani abunda kuma zamu iya fahimta harwayau shine duk irin badakalar da aka shirya a zamanin PDP a jihar Bauci yuguda yana da kaso a ciki ,yayi shekara takwas cikin jam'iyar hasalima za'a iya fahimtar cewa gogaiya suke da Amadu mu'azu kan jagorancin jihar , don koda sabanin da ke tsakaninsu ya baiyana a sarari har gamagarin jam'iya suka fahimta sai ya baiyana cewa daman don Isa yuguda suke jam'iyar ba don mu'azu ba , wannan kuwa baya rasa nasaba da irin sake hanu da facaka da ya kware kai, sannan ba wanda ya isa ya wanke Isa dangane da irin murdiyar zaben 2003 wanda shi yaki a masa 2007 ,
ah ashe ba dadi ?!

wata tsaka mai muya da malam Isa ke fuskanta ita ce matsalar 'Yan -sara -suka duk da cewa sun dasu kuma suka ciro a mukumar Alhaji mu'azu to amma a hukumar malam Isa sun riga , sara da sassaka baya hana su toho .

Amma ko ba komi kamar yadda malam Abubakar gero ke cewa " Da bakikkirin gwara baki-baki "

Naku Alkalami.

Sawun giwa ne ya taka na rakumi !

Cikin lokacin da nauki tsawon lokaci ban ba blog abinci ba , nakan leka blogs din yan'uwa inga wasu maudu'ai da ya kamata ince wani abu akai , amma yanayi irin na jarrabawa bazai banni in rubuta koda wata karamar makala ba , amma yanzu Allah ya kadara mun kammala jarrabawa , giwa ta daga sawunta daga kan na rakumi

Naku Alkalami

10.4.08

Hukumar Iran ta zartar da hukuncin kisa kan malaman sunnah har lahira

Daga cikin muzgunawa da hukumar iran ta ke wa ahlussunah , kullum
ana ganin sabon abun ban mamaki gashi kwanannan ta halaka sheikh Abdul
Kuddus mulazihi da sheikh Muhammad yusuf sahraby bayan an gurfana dasu
a kotu (mahakama) r garin Zahedan , shi dai malam Abdulkuddus
shine shugaban wata makaranta mai suna Darul furkan a birnin Iranshahr
dake yankin Bulushistan .
An kame malaman ne bayan musayar wuta tsakanin sojojin hukuma da
dakarun Jundullahi.
kamar yadda kafar sadarwa ta Ahlussan na Iran tayi bayani cewa
dakarun hukuma ta bisne su ba tare da mika gawauwakinsu ga iyalansu ko
yan'uwansu Ahlussunna ba.
A gefe guda kuma an gurfanar da limami mai huduba a masallacin
Ahlussunnah a garin Azad-shahr , an gurfanar da shine da laifin fito
na fito da hukuma , da kushe malaman mazhabin shi'a kan cin mutuncin
daukacin sahabban manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi da uwar muminai A'isha Allah ya kara mata yarda , da
kuma laifin hana jama'a ziyartar hubbaren shehunan shi'a don
neman tabarruki .
fassara daga :
http://www.islammemo.cc/akhbar/arab/2008/04/10/62249.html

21.3.08

In 'yan Nijar shigen Nasara ne to 'yan Najeriya shigen yahudu ne !!!!!!!!

Ba shakka koyau kasuwa tau watse baturen mulkin mallaka yai riba matuka, haba jama'a daga sharhin littafi an koma muzgune-muzgune , wai har dan arewacin Najeriya zai zagi dan NIJAR ko akasin haka? !

In bamu yaudari kammu ba zamu gaya wa akammu gaskiya cewa kowace al'umma tana da hali irin nata , bayarbe yana da matukar kabilanci , bafillatani yana da kunya , inyamuri yana son kudi kamar yanda yake son 'ya'yansa koma fiye shi kuwa, shi kuwa bahaushe mai matacciyar zuciya ne , ta inda baisan yayi aiki mai kare mutunci ba shi dai ya samu jin dadin rayuwa da gaggawa , shan yanzu maganin yanzu , duk kuwa wanda yake so yasan waye bahaushe ya kamata yazo sudan , ya gani wallahi yahudun zamanin HITILA sun fisu kima , ga bara da roko da karuwanci da tsibbu da sata , abun mamaki har , wasu alhazaine ke dauko yara ta hanyar rudin iyayansu , su kawo su nan sudan suna bara , kuma dole kullun sai yaro ya kawo masa abunda zai daidai , da N5000 (dubu biyar) , in kuwa bai kawo daure shi za ayi da sarka a daki a tara masa gajiya , kuma ni bahaushe nace akwai yan najeriya akwai yan Nijer .
banga dalili da wani bahaushen Najeriya zaiwa dan nijer tinkaho dashi ba , Fetur ne ! amma ya zama kwalelenka , masu tsotsa nayi mu kuwa sai kallo a NTA .
Duk wanda yasan najeriya musamman kano jalla babbar Hausa yasan irin kaba'iran da akeyi wanda ya sabawa hankalin dan'adam , wanda ba dadin fadi wai ace har anyi bukin auren mace da mace a kano , ga wata matsalar ta 'yan luwadi a bauci , ina ganin manzon Allah cewa akai masa ya fara gargadi da iyalan sa na kusa , to shawarar da zan wa kowani marubuci kafin ya tsallaka ya dauko matsalolin kasashen waje ya fara da matsalolin Kanon da ba irin sabon Allah da babu ciki , karuwanci , bokanci , tsubbu, luwadi da madigo wanda muka sani da wanda bamu sai ba , sannan yayi kan wudil ko Bauci.

Galibi in ana maganar talaucin kasa ko tattalinnta to wannan zai sa mushiga batun siyasa da mahukunta , don ALLAH tambaya waya kashe Najeriya kudu da arewa in ba bahaushen arewa ba , waya saci dukiyar najeriya fiye dashi , waya kashe ilimi ? , bahaushe ne ! waya tattari kudi ya kai kasar waje ? , ba shakka batun da wani yayi kan cewa tun mutuwar Ahmadu Bello , komi ya lalace gaskiya ne !

Malam Dankwairo yana cewa :

yan arewa ga ranar sardauna
kuyi aniya yayan sardauna
kumai da himma ku dauke girma


to amma ina ! malam dankwairo ai daga mutuwar Gamji dankwarai wasu yan hausa fim suka dawo .
Bai taba halatta ga wani dan arewacin najeriya ya aibata wani a duniya ba , saboda dukkan aibi da abun kunya yana ga bahaushe musulmin najeriya , tunda a garin Abubakar tafawa balewa ne aka yi kisan kiyashi wa musulmai , akayi a jos , kafancan , zangon kataf , lantang a daidai lokacinda bahaushe ya kule wajen iya taka rawa da waka a hausa fim wanda ba abunda ya jawo face lalata yara manyan gobe , da sunan adabi , basu san duk adabin da ba ladabi shirme bane .
Don ALLAH ka fadi mun in bahaushe bai hana kashe dan'uwansa musulmi a arewa ba to me zaiyi in ana kashe a kasar inyamurai , idan har wai wasu zasu ce Nijer jahila ce to ai suna da uzuri , mu masana meye uzurinmu ?
ya kamata mu gane dalilin da Allah yafi fushi da yahudu fiye da nasara , su yahudu suna da matukar ilimi amma sukai fatali sanin da Allah ya basu , sukai ta bin son zuciya shi yasa Allah yace musu " magdhubi alaihim" wato wadanda akai fushi dasu, su kuma nasara jahilai ya kira su da " Addhaleen" wato batattu.

wani abu da nake so jama'a su fahimta shine , tun zamanin juyin faransa wato (french revolution) har yau ba kasar duniya da ta bawa mace 'yanci ko hakki, tunda a mahaifar juyin faransa aka hana mata musulmai sa hijabi , ko su ba mata bane? , kai a BAUCI nasan makarantar da har yau mace bata da damar sa hijabi , kuma bari mugani zamu tabbatar cewa akwai hakkin mace idan Hillary Clinton taci zabe a amurka dukda cewa , jamiyar jamhuriya ta bush ta sanya amurka a bala'i don haka ba'a tsammanin wani zai zabi wannan shu'umar jam'iya, dukda cewa Barrack Obama baki ne , sannan ubansa musulmi ne , sannan ita clinton tana da uwa a murhu tunda mijinta yayi zaman farin gida ita kuwa ba lokon da bata sani ba, to ku marubutan hausawa idan har taci nasarar zama shugaba to na yarda akwai wani a abu a wayewar bature mai suna 'yancin mace .

shin 'yan'uwa kunsan 'yancin mace ga yammacin duniya ?

to in baku sani ba shine karuwanci da tallace-tallacen a gidan talabijin , saboda in har aka yarda aka nuna mata 'yan cinta kamar yadda musulunci ya nuna to fa mazinata maza sun shiga uku don baza su sami nishadantuwa dasu ba , saboda zasu yi aure kuma ba wawan da zai yarda ya auri mace wani ya ringa masa yankan baya , don haka ni ba mace uwa , kanwa , ya , kaka ba , ko kiyashi ne aka zalunta ina goyon bayan ya nemi hakkinsa , amma ta yaya ? ? ?

finafinan hausa ma jawabi ne , mai hankali ke ganewa !!!!!

Naku Alkalami

7.2.08

Shi wannan ba ta'addanci bane

Ba shakka satar yaran dafur da wata kungiyar jinkai ta faransa tayi ya wuce a kafofin watsa labarai kamar shafa labari shuni amma ba shakka ga dukkan mai hankali wannan abu zai saura a tunaninsa har sai ya fahimci meye ma'anar ta'addanci a fahimtar yammacin duniya
Ba shakka wannan nasaran da Allah ya jarrabi dan afurka dashi bai dakatar da mulkin mallaka ko bautar da bakin fata ba kamar yadda wasu suke cewa ai ya koma bautar da hankulan bakin mutun ne to har yanzu suna da abun da suke kira White slavery in zai yuyu a hausa muce farar bauta wacca wannan satar yara daga dafur da chadi yana daga ciki hakan kuma sun yi shi ne domin 1 karuwantar da su 2 kiristar da su 3 yanke musu wasu gabobi domin bawa turawa mara sa lafiya,kamar koda, to don Allah ina jinkai da mutantakar da Allah ya saka a zuciyar duk wani abu mai rai idan ya zama dan afurka musulmi ba masa kallon cikakken mutum innama shi dan adan a mataki na biyu.

Wannan mas'ala kuwa ta wuce mai tambayarta tun lokacin da shugaban faransa ya zo yayi kutun-kutun ya sa aka saki wadannan masu laifin wanda Wannan waki'a ta baiyana gaskiyar masu cewa wadannan kungiyoyin jinkai na yammacin duniya suna da ajandodi boyaiyu ba wai nufinsu shine jin kai ba

In bamu mance ba yammacin duniya sunyi ruwa sunyi tsaki wajen rufe wasu kungiyoyin musulunci da rufe musu asusun bankunansu wai suna tallafawa ta addanci, sannan suke hana gungiyoyin jinkai na musulunci wuraren da bala'I ya dauka musu don su kiristartar da wanda suka so ba tare da ja'inja ba

6.2.08

ALLAH JIKAN MALAM BAKAR ABU ZAID


Malam bakar abu zaid ya rasu ranar talata 25/1/1429 h wanda yayi daidai da 5 / 2 / 2008m an haife shi ne kuwa 1365h .
sheikh Ahmad [mijin yarsa ] shine ya jagoranci masa salla kamar yanda malam bakar yayi wasici , sallar kuwa ta sami halartar sheikh Abdul-Aziz bn Abdallah Ali sheikh da sarakuna da dalibai da masoyan malamin , hat tituna da hanyoyi suha cika saboda jama'ar da suka kai gawarsa har makabartar Dir'iyah .


Malamin ya fito ne daga gidan mutunci da dukiya , yayi karatun allo sannan ya shiga firamare , ya sami karasa karatunsa tun daga wani bangare na karatunsa na firamare sannan ma'ahad ilmy da sannan tsankayar karatun shari'a da babbab makarantar alkalanci a birnin Riyadh , a gefe guda kuma yana gurfana gaban shehunnan malamai don neman ilimi a zaurukansu , ya karanci luga ga malam salih bn Abdullahi bn mutlaq tsohon alkali a Riyadh har saida ya hardace makamomi ashirin da biyar daga makamakamatul hariry da sharhinsu na Abul Abbas assharbashi a gabansa.

sannan ya lizimci sheikh Abdul-Aziz bn baz [ Allah ya rahanceshi] ya karanci abubuwa da dama a gunsa daga ciki hadda bangaren aikin hajji da cikin littafin Almuntaqa a masallacin makkah , sannan ya dau ilimi gun malam muhammad al-amin asshanqidy inda ya karanci tafsirinsa adwa'ul bayan da juzu'i na farko a cikin littafin labbun bincike da jayaiya da usulul fikhi da ilimin dangi a massallacin madinah da gidansa.
An nada shi alkali a babban kotun madina ya zama malami a masallacin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi bayan haka da shekara daya ya zama wakili a ma'iakatar shari'a [ ministry of justice] , ya kuma zama jakadan sa'udiya a majma'in fikihu na kungiyar hadin kan duniyar musulunci, yana cikin dauwamammen komiti na bincike da fatawa.
Lokacin da yake alkalanci ne ya ci gaba da karatu daga nesa har ya same shaidar masta da dakta .
malam bakar abu zaid ya wallafa littatafai kamar hamsi an buga wasu daga ciki akwai


1-ابن القيم . حياته ، وآثاره ، وموارده .
2 – التقريب لعلوم ابن القيم .
3 – فقه النوازل . مجلدان .
4 – معجم المناهي اللفظية .
5 – طبقات النسابين .
6 – معرفة النسخ الحديثية .
7 – التحديث فيما لا يصح فيه حديث .
8 – حلية طالب العلم .
9 – التعالم .
10 – الرقابة على التراث .
11 – تعريب الألقاب العلمية .
12 – آداب طالب الحديث من الجامع للخطيب .
13 – التراجم الذاتية من العزاب والعلماء وغيرهم .
14 – تسمية المولود .
15 – عقيدة ابن أبي زيد القيراوني والرد على من خالفها .
16 – تصنيف الناس بين الظن واليقين .
17 – حكم الانتماء .
18 – هجر المبتدع .
19 – التحذير من مختصرات الصابوني في التفسير .
20 – براءة أهل السنة من الواقع في علماء الأمة .
21 – خصائص جزيرة العرب .
22 – جزء في مسح الوجه باليدين بعد الدعاء .
23 – جزء في زيارة النساء للقبور .
24 – بدع القراء .
25 – لا جديد في أحكام الصلاة .
26 – تحقيق كتاب " الجد الحثيث في بيان ما ليس بحديث " للعامري .
27 – تحقيق اختيارات ابن تيمية للبرهان ابن القيم .
28 – أذكار طرفي النهار .
29 – تحريف النصوص .
30 – المثامنة في العقار .
31 – آداب الهاتف .
32 – أدب الثوب والأزرة .


16.1.08

SHIN MATA ZA SUYI FATAN DUKIYA GA MAZAJENSU KUWA?



Wani labari da na taba karantawa kan wani nasara da ya shiga mota zaiyi kaura ya bar garinsa , bayan motar ta dau hanya sai zumbur kamar ya tuna da wani abu , ya jawo jakarsa ya bude sai ya ciro rigarsa da wando da malafa {Hat}, yayi watsi da su ta tagar mota, mamaki ya game jama'ar cikin motarnan , suka kasa hakuri suka tambaye shi, sai yayi bayanin cewa ya kauracewa matarsa ne yana so ya sake sabuwar rayuwa don haka yake yasarda duk abunda zai sa ya iya tunawa da ita .

Abun da nake so nan mu fahimta shine mutum zaiso rabuwa da duk wani abunda zai tuna masa wani kunci ko matsi ko damuwa da ya taba shiga.


To amma wani abu shine mace zata iya zama abun da za'a yasar don kar a tuna da wani yanayi da aka taba shiga na kunci musammam talauci kamar yadda wancan Nasara ya zubar da tufafinsa kuma dama Allah ta'ala cikin kurani ya kira su tufafi inda yacewa maza : [[ su tafafi ne a gareku , kuma kuma tufafine a garesu ]] suratul bakarah , ayata 187.

kamar yadda muka saba gani yayin da Allah ya budewa namiji kofofin arziki bayan ya shekara saba'in cikin talauci abunda zai fara yi shine zai tashi haikan don kauda duk abunda zai tuna masa da kwanakin talauci , don haka zai gina sabon gidan sama don kauracewa gidan kasa, ya sayi sabuwar mota don rabuwa da keke koma saiyada {sawu} ya auro sabuwar budurwa don ya bar matarsa ta fari uwar 'ya'yansa wacca suka zauna zaman hakuri da tawakkali ,

Wani mutum daya halarci wata liyafa da wani alhaji sabon kudi ya gaiyace shi yana cewa {{……bayan mun kammmala wannan liyafa wacca tana daga cikin manyan liyafofi dana taba halarta a rayuwata , abokan alhaji attajirai da 'yan siyasa suna masa bankwana da barka kan sabuwar budurwar amarya da yayi wanda shine sanadiyar wannan shagali , wasu ma sun ja motocinsu sun yi gaba sai ga wata mace marabanta da mabaraciya kadan ne tana kira ga alhazannan da su taimaketa su isar da sakonta zuwaga mai gidan , tana cewa itace matarsa shekaru arba'in da suka gabata saidai tun sanda ya fara samun kwangila a hukumar jiha da ma ta taraiya sai ya fara sauya salon mu'amala da ita , yana takalar fada don in ta mayar masa da martani ya sallame ta, hakan kuma akayi , ta kara da cewa yanzu haka wannan yaron da ke hanuna karamin dansa ne na zo karba masa hakkinsa amma masu gadi sun hana ni shiga , saboda basu santa ba, kuma dama bai taba yin masu gadi ba sai da Allah ya masa fatahi , don haka bazasu sanni ba, wannan mata ta karkare wannan bayani nata da wani matsakaicin kuka da tayi ta kokarin matse shi amma yaki . hawaye kuwa yana zuba car car daga idanunta , wasu daga cikinmu masu tausasan zukata suma suka kasa tsantsame hawayensu.}}

wannan dabi'a ta namiji yasa nayi shakkar matan aure suyi fatan Allah ya ya tarfa wa garin mazajensu nono, amma kai me ka/kika gani?


6.1.08

BENAZIR BHUTO DA GUNKIN DABINO


Bilawal Bhutto dauke da hoton marigayiyar


Sau da dama wannan zamani yana kawo wasu wakoki da ake rerawa da har yanzu wasu wanda ni ma Alkalami ina daga cikinsu mun kasa gane hakikanin ma'anarsu , mu samman wakar nan ta Dimukuradiya wanda na hakikance cewa kidine kawai akeyi ake rausayawa , amma ba wata kalma ko jumla ciki bare a fahinci manufarta.

ku yafeni ya ku mabuga tamburan dimukuradiya in abun bai muku dadi ba , amma yadda ya wajaba in nunfasa haka kuma ya wajaba in baiyana irin wannan rainin hankalin da nake ji a cikin kade kaden dimukuradiya .

Allah yayi cikawa wa malama Benazir Bhutto tsohuwar firayim minista kuma 'ya ga tsohon firayim minista Zulfikar Ali Bhutto wanda ita da mahaifinnanta duk mabiya tafarkin shi'a ne , a yanzu dai ana kokarin ganin binciko wadanda suka yi wannan buruntu, inda shugaba Pervez Musharraf ya daura alhakin wannan kisan gillan ga Alka'ida saboda ita bhutto ta sha lasan takobin murkushe an alka'idan , sannan kuma suna ganin itace takeda cikakken goyon bayan amurka da yan barandanta fiye da kowa a pakistan saboda shi musharraf namiji ne kuma soja don haka akan samu tangarda dashi , baya bi a makance , sannan a bangare guda kuma za'a iya tuhumar shi musharraf din saboda jagorancin da take yi na kokarin kadashi a zabe mai zuwa.

Abunda ya ja hankalina kan wannan waki'a shine yanda dimukradiya ta dawo gunkin da akayi shi da dabino , in aka koshi ayi masa sujjada in kuma aka ji yunwa a ringa gutsura anaci , ta inda ita bhutto ta bar wasiyar a daura danta Bilawal Bhutto dan shekara 19 wanda yake karatun tarihi a jami'ar Oxford kan karagar jam'iyar Parkistan People Party { PPP} , wanda shine kenan zai fito takara da Musharraf , shi kuma mahaifinsa Asif Ali Zardar mataimakinsa. haka nan shugaba Gaddafi {dukda cewa shi ba kan tsarin dimukuradiya yake ba , amma jamhuriya ne ba mulukiya ba} yana neman daura dansa Saiful-islam kan mulki bayansa , haka ma shugaban masar mubarak nufinsa kenan, marigayi Hafez Asad shima ya daura dansa Basshar Al-asad a Syria .

Abun mamaki jaridar Almizan dangane mulukiyar Benazir Bhutto cewa tayi :

''
A yayin da kasashen duniya ke ta kiraye-kirayen a samar da wani kwamitin bincike na kasa-kasa da zai binciki masu hannu a harin da aka yi wa Bhutto, tuni har jam’iyyarta ta zabi danta da mijinta a matsayin wadanda za su ci gaba da jan ragamar jam’iyyar don fuskanta zaben da ke tafe ''.
zaka iya karanta wannan rahoto nasu a yanar gizo ta wannan adreshi http://www.almizan.net/bls803c.html, alhali kuwa shafin yanar gizo na malama Bhutto ya tabbatar cewa gadar wa danta da mahaifinsa tayi in da ya baiyana cewa :

'' Benazir Bhutto's 19-year old son has been appointed chairman of his late mother's opposition political party in Pakistan.

Bilawal Bhutto, who is reading history at Oxford, will chair the Pakistan People's Party with his father, Asif Ali Zardar, as co-chairman.

Bilawal Bhutto right, being comforted by his father Asif Ali Zardar. Party officials made the announcement after the reading of Miss Bhutto's will following her assassination last week.'' , za kuma a sami wannan a cikin shafinta mai adreshin http://www.benazirbhutto.co.uk/Default.php

to abun tambaya ko me yasa yan shi'an basa so ace gadarwa tayi , Allahu a'alamu!


wannan na nuna cewa yanzu ma'anar dimukuradiya ya tashi daga hukumar jama'a zuwa hukumar gado kuma koda magajin karami ne dan shekara shata tara .

wannan bazai bada mamaki sosai ba idan muka tuna cewa Amurka su suka fara taya Moi Kibaki murnar komawa kan mulki dukda sun san cewa bashi ya lashe zabenba , amma tunda sunsan ba dole ne Odinga ya sake musu kamar yadda kibaki yabari suka ringa diban musulmai suna kaiwa Gwantanamo ba da sunan ta'addanci, sannan baza mu mance cewa Hamaz suka ci zaben palasdinu ba, amma turai gaba daya suka juya musu baya suka ringa azabtar da jama'ar da yunwa saboda basu zabi wadanda su { turai } suke so ba wato Fatah .
Allah yayi gaskiya da yace '' yahudu da Nasara basu yarda da kaiba harsai kabi tafarkinsu ''