15/shauwal/ -h _26/11/2007
Malam Kabiru Yakasai ba shakka haziki ne mai matukar hikima , da alama kuwa hannunsa ya jima yana goga alkalami kan takarda .
Duk wannan takaitaccen yabon ba wai nasan shi bane , saidai na kwatanta zakakurancinsa ne sakamakon karanta littafinsa mai suna ‘’suda’’ littafinda ya hada nishadantarwa da tarbiya da azanci .
Shekaran jiya nake karanta shi lokacinda na bakonci dangina a omdurman na jamhuriyar sudan , amma lokaci zuwa lokaci sai in kyalkyale da dariya saboda in nayi hakuri a taran aradu da kan dankani wani lokaci to wani lokacin kuma bazan iya hana bakina ‘yancin dariya ba.
Mun kasance muna kishirwan mawallafa irin malam Kabiru ruwan wankin daudar zamantakewa , don kuwa mun kosa da masu kwashe baiwar talifi da Allah ta’ala ya musu sui ta yawo tsakanin so da ki , da soyaiya da kiyaiya kamar mu hausawa wata al’umma ce wacca bata da wata matsala sai soyaiya .
Malam ya fara bada labarin baba suda a takaice wanda shi kuma shine ya ba yara labarin rigingimun dankane, kuma ni a fahimta ta malam ya nusar damu ne cewa tara yara da basu labaru wata hanyace ta tarbiya , kamar yadda Allah ta'ala ya dauki wannan salo a kaso mai girma na Alkur’ni kamar : suratu Yusufa kacokam dinta ta bada labarin annanbi yusufa ne , ta kuma bada mahimmanci kan al’amuran zamantakewa ,wasu surori kuma annabi Isa , Musa , Dauda da Sulaiman , Ibrahin da sauransu , da labarin sarakuna kamar Fir’auna da Lamarudu , duk wannan domin mu dau izna .
Wani abu mai tabbatar mana cewa mawallafin ya na da hadafin azo agani wajen talifin wannan littafin shine inda yayi bayanin cewa baba suda ya bawa yara wannan labarin ne saboda ya umurci wani yaro da ya sai wa alkaki da ya samma dan’uwansa da ya makara bai samu ba , sai yaron yaki daga nan sai ya kwabe su da su bar rowa daga nan ya fara basu labarun wahalhalun da dankane ya sha wanda galibinsu sakamakon rowarsa da son kudinsa ne kamar dan canjin yahudawa.
Mawallafin yayi bulala wa sharifan karya dama na gaske masu ci da salsalar nasaba , yan danfara , barayin zaune , sannan yayi bayanin yadda dankane ya tashi daga almajiri zuwa matsayin alkali zuwa waziri har sanda yayi juyin mulki ya dawo sarki mai cikkakken iko daga nan kuma yayi karkon kifi ya koma tunku , abun mamaki!! .
Sannan yaci gaba da tsumage ‘yandaudu da malaman tsubbu 'yan kawo rago kawo zakara mai kwai, da masu ruwan ido , har lokacinda dankane ya ga ba harkar da bai shiga ba amma bai ci nasara ba saura masa harka daya da bai jarraba ba itace harkar kamun kai da bin addini sauda kafa , daga nan ya yasar da duk wani shashanci har ma ya koma alaramma mai jan baki a ramalana.
Saidai malam kabiru abunda ya daure mun kai wai shin akwai wani nassi daga kur’ani ko hadisi mai tabbatar da cewa sharu wuta bata kama shi koko dai siddabaru da rufa ido sharifan suke yi ? .
Har wayau aganina ba kai tsaye ba ka daurewa bokaye da malaman tsubbu gindi in da kayi bayanin wani malami mai gudun duniya ya ba dankane wuridin kiran aljanu to amma wannan malamin ba kamar yanda kayi bayani cewa malamin Allah da annabi bane tunda wannan shirka ne hada Allah da wani ne , Allah kuwa yana cewa ‘’ idan bayina suka tambayeka dangane da ni to ni a kusa nake ina amsa kiran mai kira in ya kirani ’’
Wani abun da na lura dashi kan littafin ‘‘ suda‘‘ shine jama’a sunfi saninsa da ‘‘Dankane‘‘ , sai naga dama malam kabiru ya rada wa littafin Suna DANKANE , sannan kalmar dankane wani sa’in malam yakan sa mata wasalin [e] wani lokaci kuma wasalin {I} tsammanina so yake ya nusar da mu cewa duka hausa ce karbabbiya dankani da dankane.
Zanso ku karanta littafin SUDA sai dai kar ku zargi malam kabiru idan bakin ku ya barke don dariya.
Wassalam.