17.12.07

HAPPY EID -UL- ADHA

8.12.07

WALIDAINI

Ina zaune karkashin inuwar la'asariya , duk damuwata wata ya kusa faduwa gashi ban sa wani rubutu da yake matsayin abinci ga BLOG dina kamar yadda nasara suka kira shi , ko MUDAUWANA inji larabawa adaidai lokacinda naga wani bahaushen ya ambaceshi TURAKA , wanda ni tawa turakar na mata inkiya da ALKALAMI saboda na fahimci zamanin tsinin mashi, ko kibiya, ko roka , ko allura ya gushe yanzu lokacine na tsinin alkalami.

Ina cikin murza alkalamina a tsakanin hakora don tuna guzurin da zan kawo wa masu sai ga wani abokina sa'idu yana tafiya jikinsa a mace kamar bai da laka duk ayoyin bakin ciki suna karantuwa a fuskarsa kai harma da surori.

Saidu lafiya kuwa kake tafe kana raba hanya kamar kasha ruwan bagaja ?
na kamo hanunsa na zaunar dashi kan dakalin gidanmu

'' ai ka bari kawai dama giya nasha ai da da sauki don kuwa cutarta daga ni sai ni''

to me ya faru me ka rasa bayan kana karbar albashin da bai gaza dubu arbain ba.
Bayan dogon rarrashi sai ya kada baki yace :

"Mahaifiyata ta rikeni a cikinta tsawon wata tara, jininta yana gudana tare da jinina , harna zame mata tamkar wata gaba daga jikinta, sannan ta zaroni daga cikinta kamar tana zaro ranta , da na sauko duniya kuwa ba abunda ke sata murmushu kamar murmushina , kamar yadda ba abu mai sata kuka kamar kukana, ta bani nonota na tsotsi rayuwata daga cikinsa, yayinda kuwa nayi zazzabin hudowar hakori sai barci ya kaurace masa ta kuma mance dandanon abinci, ta hana kanta dadadan abubuwa domin ta bani , ta yunwata domin in koshi, kai Alkalami ba abunda nake tunawa kamar randa ta kwashi uwar jari da ribar kulikulinta ta saya mun adaka da garin rogo da sukari da tsintsiya da fartanya zan tafi makarantar kwana , ita kuwa ta zauna hanu banza , nazo tafiya tana hawaye wai don zan gamu da yaran masu hanu da shuni ana kawo musu ziyara a motocin alfarma , a kawo musu madara da biskit da kanzon kwali dama abunda banji ba, ban taba gani ba, ban kuma taba darsa shi a tunaniba.

Shiko mahaifina bai tada fashin zuwa jeji ba komai sanyi komi zafi , tun hantsi kuwa in ya riki gatari sallar azahar ce ke sa ya saki, ya debo abun da ya samu , ya dawo gida kewaye da abubuwa uku yunwa da kishi da gajiya, amma ba abunda zai tarwatsa masa kan wannan musallasi sai sautina yayin da nace OYOYO BABA ! nayi watsi da wasan da nake yi na sheko da gudu shi kuma ya daga ni sama ya jijjiga cikin farin ciki.

Lokacin da na gama makaranta da sakamakon da ya ban damar shiga jami'a gashi lamari ne mai bukatar kudi, gonarsa ta kusa da makabarta ya sayar don biya mun abunda ya jawo masa zagi da zunde da kifce da yafuce a kauyemmu cewa ga wanda ya tozarta NA DUKE TOSHON CINIKI don dansa yayi karatun nasara asarar duniya, wasu ma har .......""

Nan take na katseshi nace : " sa'idu wai meye alakar wannan dogon jawabi da damuwarka , ai falalar iyaye abune a baiyane kamar wata daren sha hudu , da zaka ji wahalar da iyayena suka sha kaina da baka iya hana hawaye tsirarowa da idanunka ba, shi yasa nake musu carafken kwai kan kanfa."

Saidu ya ce '' ai in gaya maka ban taba jin kwakwalwa a kaina ba saida na ganni a kotu ''

Nan take nayi zumbur nace '' me ya kaika kotu? wa ya maka kazafi ? yanzu a garinnan har an fara yiwa mumunai kage? ''

Sa'idu yace '' mahaifana nane suka kaini gaban alkali don ya karba musu hakkinsu , saboda basu da karfin yin aikin karfi kuma gashi suna bukatar abunda zasu ci''

nace '' to ina makudan albashin da kake karda daga bankin al'umma ? ina suke tafiya? "

yace yanzu " yanzu Alkalami ka mance yanda muke da Biba , yariyar nan kamar ta daure ni da guru "
Nace " A'a ka daure kanka dai, yo imma da hanun boka ta daure ka , ina Aayatul kursiyu da kula'uzai ? "

Ya kara da cewa" ai in gaya maka in har na damki kudin nan bana iya zarcewa ko ina sai gidansu Biba, in damka mata tayi kasafin wannan wata , ta yafuta mun kadan da zanci garau-garau"

Yaci gaba da cewa yanzu haka alkali yadaga sauraran karar zuwa mako mai zuwa , so nake inje in roke su su janye karar , in nemi gafarar su, amma fa kar ka gayawa kowa , don na sanka"

Nace :" in banda kai ka taba ji Alkalami tona asiri ? "