Ba shakka koyau kasuwa tau watse baturen mulkin mallaka yai riba matuka, haba jama'a daga sharhin littafi an koma muzgune-muzgune , wai har dan arewacin Najeriya zai zagi dan NIJAR ko akasin haka? !
In bamu yaudari kammu ba zamu gaya wa akammu gaskiya cewa kowace al'umma tana da hali irin nata , bayarbe yana da matukar kabilanci , bafillatani yana da kunya , inyamuri yana son kudi kamar yanda yake son 'ya'yansa koma fiye shi kuwa, shi kuwa bahaushe mai matacciyar zuciya ne , ta inda baisan yayi aiki mai kare mutunci ba shi dai ya samu jin dadin rayuwa da gaggawa , shan yanzu maganin yanzu , duk kuwa wanda yake so yasan waye bahaushe ya kamata yazo sudan , ya gani wallahi yahudun zamanin HITILA sun fisu kima , ga bara da roko da karuwanci da tsibbu da sata , abun mamaki har , wasu alhazaine ke dauko yara ta hanyar rudin iyayansu , su kawo su nan sudan suna bara , kuma dole kullun sai yaro ya kawo masa abunda zai daidai , da N5000 (dubu biyar) , in kuwa bai kawo daure shi za ayi da sarka a daki a tara masa gajiya , kuma ni bahaushe nace akwai yan najeriya akwai yan Nijer .
banga dalili da wani bahaushen Najeriya zaiwa dan nijer tinkaho dashi ba , Fetur ne ! amma ya zama kwalelenka , masu tsotsa nayi mu kuwa sai kallo a NTA .
Duk wanda yasan najeriya musamman kano jalla babbar Hausa yasan irin kaba'iran da akeyi wanda ya sabawa hankalin dan'adam , wanda ba dadin fadi wai ace har anyi bukin auren mace da mace a kano , ga wata matsalar ta 'yan luwadi a bauci , ina ganin manzon Allah cewa akai masa ya fara gargadi da iyalan sa na kusa , to shawarar da zan wa kowani marubuci kafin ya tsallaka ya dauko matsalolin kasashen waje ya fara da matsalolin Kanon da ba irin sabon Allah da babu ciki , karuwanci , bokanci , tsubbu, luwadi da madigo wanda muka sani da wanda bamu sai ba , sannan yayi kan wudil ko Bauci.
Galibi in ana maganar talaucin kasa ko tattalinnta to wannan zai sa mushiga batun siyasa da mahukunta , don ALLAH tambaya waya kashe Najeriya kudu da arewa in ba bahaushen arewa ba , waya saci dukiyar najeriya fiye dashi , waya kashe ilimi ? , bahaushe ne ! waya tattari kudi ya kai kasar waje ? , ba shakka batun da wani yayi kan cewa tun mutuwar Ahmadu Bello , komi ya lalace gaskiya ne !
Malam Dankwairo yana cewa :
yan arewa ga ranar sardauna
kuyi aniya yayan sardauna
kumai da himma ku dauke girma
to amma ina ! malam dankwairo ai daga mutuwar Gamji dankwarai wasu yan hausa fim suka dawo .
Bai taba halatta ga wani dan arewacin najeriya ya aibata wani a duniya ba , saboda dukkan aibi da abun kunya yana ga bahaushe musulmin najeriya , tunda a garin Abubakar tafawa balewa ne aka yi kisan kiyashi wa musulmai , akayi a jos , kafancan , zangon kataf , lantang a daidai lokacinda bahaushe ya kule wajen iya taka rawa da waka a hausa fim wanda ba abunda ya jawo face lalata yara manyan gobe , da sunan adabi , basu san duk adabin da ba ladabi shirme bane .
Don ALLAH ka fadi mun in bahaushe bai hana kashe dan'uwansa musulmi a arewa ba to me zaiyi in ana kashe a kasar inyamurai , idan har wai wasu zasu ce Nijer jahila ce to ai suna da uzuri , mu masana meye uzurinmu ?
ya kamata mu gane dalilin da Allah yafi fushi da yahudu fiye da nasara , su yahudu suna da matukar ilimi amma sukai fatali sanin da Allah ya basu , sukai ta bin son zuciya shi yasa Allah yace musu " magdhubi alaihim" wato wadanda akai fushi dasu, su kuma nasara jahilai ya kira su da " Addhaleen" wato batattu.
wani abu da nake so jama'a su fahimta shine , tun zamanin juyin faransa wato (french revolution) har yau ba kasar duniya da ta bawa mace 'yanci ko hakki, tunda a mahaifar juyin faransa aka hana mata musulmai sa hijabi , ko su ba mata bane? , kai a BAUCI nasan makarantar da har yau mace bata da damar sa hijabi , kuma bari mugani zamu tabbatar cewa akwai hakkin mace idan Hillary Clinton taci zabe a amurka dukda cewa , jamiyar jamhuriya ta bush ta sanya amurka a bala'i don haka ba'a tsammanin wani zai zabi wannan shu'umar jam'iya, dukda cewa Barrack Obama baki ne , sannan ubansa musulmi ne , sannan ita clinton tana da uwa a murhu tunda mijinta yayi zaman farin gida ita kuwa ba lokon da bata sani ba, to ku marubutan hausawa idan har taci nasarar zama shugaba to na yarda akwai wani a abu a wayewar bature mai suna 'yancin mace .
shin 'yan'uwa kunsan 'yancin mace ga yammacin duniya ?
to in baku sani ba shine karuwanci da tallace-tallacen a gidan talabijin , saboda in har aka yarda aka nuna mata 'yan cinta kamar yadda musulunci ya nuna to fa mazinata maza sun shiga uku don baza su sami nishadantuwa dasu ba , saboda zasu yi aure kuma ba wawan da zai yarda ya auri mace wani ya ringa masa yankan baya , don haka ni ba mace uwa , kanwa , ya , kaka ba , ko kiyashi ne aka zalunta ina goyon bayan ya nemi hakkinsa , amma ta yaya ? ? ?
finafinan hausa ma jawabi ne , mai hankali ke ganewa !!!!!
Naku Alkalami
21.3.08
In 'yan Nijar shigen Nasara ne to 'yan Najeriya shigen yahudu ne !!!!!!!!
Posted by
alkalami alkalami alkalami
at
5:19 AM
12
Opinion
Subscribe to:
Posts (Atom)
