17.12.07

HAPPY EID -UL- ADHA

8.12.07

WALIDAINI

Ina zaune karkashin inuwar la'asariya , duk damuwata wata ya kusa faduwa gashi ban sa wani rubutu da yake matsayin abinci ga BLOG dina kamar yadda nasara suka kira shi , ko MUDAUWANA inji larabawa adaidai lokacinda naga wani bahaushen ya ambaceshi TURAKA , wanda ni tawa turakar na mata inkiya da ALKALAMI saboda na fahimci zamanin tsinin mashi, ko kibiya, ko roka , ko allura ya gushe yanzu lokacine na tsinin alkalami.

Ina cikin murza alkalamina a tsakanin hakora don tuna guzurin da zan kawo wa masu sai ga wani abokina sa'idu yana tafiya jikinsa a mace kamar bai da laka duk ayoyin bakin ciki suna karantuwa a fuskarsa kai harma da surori.

Saidu lafiya kuwa kake tafe kana raba hanya kamar kasha ruwan bagaja ?
na kamo hanunsa na zaunar dashi kan dakalin gidanmu

'' ai ka bari kawai dama giya nasha ai da da sauki don kuwa cutarta daga ni sai ni''

to me ya faru me ka rasa bayan kana karbar albashin da bai gaza dubu arbain ba.
Bayan dogon rarrashi sai ya kada baki yace :

"Mahaifiyata ta rikeni a cikinta tsawon wata tara, jininta yana gudana tare da jinina , harna zame mata tamkar wata gaba daga jikinta, sannan ta zaroni daga cikinta kamar tana zaro ranta , da na sauko duniya kuwa ba abunda ke sata murmushu kamar murmushina , kamar yadda ba abu mai sata kuka kamar kukana, ta bani nonota na tsotsi rayuwata daga cikinsa, yayinda kuwa nayi zazzabin hudowar hakori sai barci ya kaurace masa ta kuma mance dandanon abinci, ta hana kanta dadadan abubuwa domin ta bani , ta yunwata domin in koshi, kai Alkalami ba abunda nake tunawa kamar randa ta kwashi uwar jari da ribar kulikulinta ta saya mun adaka da garin rogo da sukari da tsintsiya da fartanya zan tafi makarantar kwana , ita kuwa ta zauna hanu banza , nazo tafiya tana hawaye wai don zan gamu da yaran masu hanu da shuni ana kawo musu ziyara a motocin alfarma , a kawo musu madara da biskit da kanzon kwali dama abunda banji ba, ban taba gani ba, ban kuma taba darsa shi a tunaniba.

Shiko mahaifina bai tada fashin zuwa jeji ba komai sanyi komi zafi , tun hantsi kuwa in ya riki gatari sallar azahar ce ke sa ya saki, ya debo abun da ya samu , ya dawo gida kewaye da abubuwa uku yunwa da kishi da gajiya, amma ba abunda zai tarwatsa masa kan wannan musallasi sai sautina yayin da nace OYOYO BABA ! nayi watsi da wasan da nake yi na sheko da gudu shi kuma ya daga ni sama ya jijjiga cikin farin ciki.

Lokacin da na gama makaranta da sakamakon da ya ban damar shiga jami'a gashi lamari ne mai bukatar kudi, gonarsa ta kusa da makabarta ya sayar don biya mun abunda ya jawo masa zagi da zunde da kifce da yafuce a kauyemmu cewa ga wanda ya tozarta NA DUKE TOSHON CINIKI don dansa yayi karatun nasara asarar duniya, wasu ma har .......""

Nan take na katseshi nace : " sa'idu wai meye alakar wannan dogon jawabi da damuwarka , ai falalar iyaye abune a baiyane kamar wata daren sha hudu , da zaka ji wahalar da iyayena suka sha kaina da baka iya hana hawaye tsirarowa da idanunka ba, shi yasa nake musu carafken kwai kan kanfa."

Saidu ya ce '' ai in gaya maka ban taba jin kwakwalwa a kaina ba saida na ganni a kotu ''

Nan take nayi zumbur nace '' me ya kaika kotu? wa ya maka kazafi ? yanzu a garinnan har an fara yiwa mumunai kage? ''

Sa'idu yace '' mahaifana nane suka kaini gaban alkali don ya karba musu hakkinsu , saboda basu da karfin yin aikin karfi kuma gashi suna bukatar abunda zasu ci''

nace '' to ina makudan albashin da kake karda daga bankin al'umma ? ina suke tafiya? "

yace yanzu " yanzu Alkalami ka mance yanda muke da Biba , yariyar nan kamar ta daure ni da guru "
Nace " A'a ka daure kanka dai, yo imma da hanun boka ta daure ka , ina Aayatul kursiyu da kula'uzai ? "

Ya kara da cewa" ai in gaya maka in har na damki kudin nan bana iya zarcewa ko ina sai gidansu Biba, in damka mata tayi kasafin wannan wata , ta yafuta mun kadan da zanci garau-garau"

Yaci gaba da cewa yanzu haka alkali yadaga sauraran karar zuwa mako mai zuwa , so nake inje in roke su su janye karar , in nemi gafarar su, amma fa kar ka gayawa kowa , don na sanka"

Nace :" in banda kai ka taba ji Alkalami tona asiri ? "


26.10.07

BIBIYAR LITTAFIN ‘’SUDA’’

15/shauwal/ -h _26/11/2007

Malam Kabiru Yakasai ba shakka haziki ne mai matukar hikima , da alama kuwa hannunsa ya jima yana goga alkalami kan takarda .
Duk wannan takaitaccen yabon ba wai nasan shi bane , saidai na kwatanta zakakurancinsa ne sakamakon karanta littafinsa mai suna ‘’suda’’ littafinda ya hada nishadantarwa da tarbiya da azanci .

Shekaran jiya nake karanta shi lokacinda na bakonci dangina a omdurman na jamhuriyar sudan , amma lokaci zuwa lokaci sai in kyalkyale da dariya saboda in nayi hakuri a taran aradu da kan dankani wani lokaci to wani lokacin kuma bazan iya hana bakina ‘yancin dariya ba.

Mun kasance muna kishirwan mawallafa irin malam Kabiru ruwan wankin daudar zamantakewa , don kuwa mun kosa da masu kwashe baiwar talifi da Allah ta’ala ya musu sui ta yawo tsakanin so da ki , da soyaiya da kiyaiya kamar mu hausawa wata al’umma ce wacca bata da wata matsala sai soyaiya .

Malam ya fara bada labarin baba suda a takaice wanda shi kuma shine ya ba yara labarin rigingimun dankane, kuma ni a fahimta ta malam ya nusar damu ne cewa tara yara da basu labaru wata hanyace ta tarbiya , kamar yadda Allah ta'ala ya dauki wannan salo a kaso mai girma na Alkur’ni kamar : suratu Yusufa kacokam dinta ta bada labarin annanbi yusufa ne , ta kuma bada mahimmanci kan al’amuran zamantakewa ,wasu surori kuma annabi Isa , Musa , Dauda da Sulaiman , Ibrahin da sauransu , da labarin sarakuna kamar Fir’auna da Lamarudu , duk wannan domin mu dau izna .

Wani abu mai tabbatar mana cewa mawallafin ya na da hadafin azo agani wajen talifin wannan littafin shine inda yayi bayanin cewa baba suda ya bawa yara wannan labarin ne saboda ya umurci wani yaro da ya sai wa alkaki da ya samma dan’uwansa da ya makara bai samu ba , sai yaron yaki daga nan sai ya kwabe su da su bar rowa daga nan ya fara basu labarun wahalhalun da dankane ya sha wanda galibinsu sakamakon rowarsa da son kudinsa ne kamar dan canjin yahudawa.
Mawallafin yayi bulala wa sharifan karya dama na gaske masu ci da salsalar nasaba , yan danfara , barayin zaune , sannan yayi bayanin yadda dankane ya tashi daga almajiri zuwa matsayin alkali zuwa waziri har sanda yayi juyin mulki ya dawo sarki mai cikkakken iko daga nan kuma yayi karkon kifi ya koma tunku , abun mamaki!! .

Sannan yaci gaba da tsumage ‘yandaudu da malaman tsubbu 'yan kawo rago kawo zakara mai kwai, da masu ruwan ido , har lokacinda dankane ya ga ba harkar da bai shiga ba amma bai ci nasara ba saura masa harka daya da bai jarraba ba itace harkar kamun kai da bin addini sauda kafa , daga nan ya yasar da duk wani shashanci har ma ya koma alaramma mai jan baki a ramalana.

Saidai malam kabiru abunda ya daure mun kai wai shin akwai wani nassi daga kur’ani ko hadisi mai tabbatar da cewa sharu wuta bata kama shi koko dai siddabaru da rufa ido sharifan suke yi ? .
Har wayau aganina ba kai tsaye ba ka daurewa bokaye da malaman tsubbu gindi in da kayi bayanin wani malami mai gudun duniya ya ba dankane wuridin kiran aljanu to amma wannan malamin ba kamar yanda kayi bayani cewa malamin Allah da annabi bane tunda wannan shirka ne hada Allah da wani ne , Allah kuwa yana cewa ‘’ idan bayina suka tambayeka dangane da ni to ni a kusa nake ina amsa kiran mai kira in ya kirani ’’

Wani abun da na lura dashi kan littafin ‘‘ suda‘‘ shine jama’a sunfi saninsa da ‘‘Dankane‘‘ , sai naga dama malam kabiru ya rada wa littafin Suna DANKANE , sannan kalmar dankane wani sa’in malam yakan sa mata wasalin [e] wani lokaci kuma wasalin {I} tsammanina so yake ya nusar da mu cewa duka hausa ce karbabbiya dankani da dankane.
Zanso ku karanta littafin SUDA sai dai kar ku zargi malam kabiru idan bakin ku ya barke don dariya.
Wassalam.

5.10.07

BIBIYAR YAKIN DUNIYA NA BIYU


A LOKACINDA JAMUS TA YAKI POLAND ,A WATAN SATUMBA 1939 ,SHEKARA ASHIRIN BAYAN YAKI DUNIYA NA DAYA , HAR ANYI TSAMMANIN ZAMAN LAFIYA YA DAWWAMA, SAI GASHI, ANGULU TA KOMA GIDANTA NA TSAMIYA, SABODA JAMUS DA JAPAN SUNYI KOKARIN BAZA MULKINSU HAR KASASHEN TURAI DA AFRICA

DA GABAS TA TSAKIYA SAIDAI SOJOJIN HADIN GWIWA SUN FAR MUSU BAYAN SUN BIYA WASU BUKATUNSU BANDA WASU ,MASU KIDAYA SUNA CEWA RAYIN MUTUM DUBU HAMSINNE YA FITA TA INDA WASU SUKACE BA A SAN YAWANSUBA.
DA GA CIKIN WAKI OIN DA ZAN IYA TUINAWA SHINE YAKINDAI YUAFARANE WATAN SATUMBA 1939 ,WATAN AFRILU HITILA ,YAYI KAFAR ANGULU GA YARJEJENIYAR SHEKARAR 1939 TSAKANINSA DA BARITANIYA, SANNANN WATAN AGUSTA NAZI TA KULLA YARJEJENIYA ZAMAN LAFIYA DA SABIYAWA SHE KUWA HITILA YAYI HAKANE DOMIN KADA RASHA TACE UFFAN,YAYIN DA ZE KAIWA POLLAN HARI,WATO HARIN DAYA KAI MATA A SATUMBA SANNAN DAGA CIKIN TUN AWA A WATAN AFRILU 1940
JAMUS TA AUKAWA DENMARK, TA INDA DA KEWAYE IYA KOKINTA ITA KUMA DENMARK TA MIKA WUYA .
A KUMA WATAN MAYU JAMUS TA KEWAYE BELGIKA A GEFE GUDA KUMA FARANSA DA BARITANIYA SUNYI KOKARIN SHIGOWA BELGIKA SAI JAMUS TA FARMUSU ,,SANNAN JAMUS TA KAMA AREWACIN FARANSA CIKIN SAUKI ABINDA YABASU MAMAKI, HAR SUKA DAKATA DA DOMAIN KARA SHIRI FARANSA DA RUNDUNARTA NAN TAKE TAFRAS MUSU/
SANNAN A WATAN YULI, JAMUS TA KEWAYE FARISA ,KUMA TA KEWAYE TSUBURIN CHANEL, A WATA MAI ZUWA KUMA HITILA YA UMARCI RUNDUNARSA DA AUKAWA BARITANIYA
WATA BABBAR WAKIM A KUMA ITACE HARE HAREN SAMA MASU GIRMA WANDA JAMUS TA ZAZZAGE A BIRNIN LONDON,ITAMA LONDON DA DAU FANSA WANDA BAIKAI NA JAMUS BA.
CIKIN SHEKARAR 1941 WATAN YULI,KWATSAM SAI YARJEJENIYAR TSAGAITA KAWO HARI,TA KARE TSAKANIN JAMUS DA SABIYAWA,YAYINDA JAMUS TAKAI MUMMNAN HARINDA TARIHI YA BUGA MASA HATIMI.
SANNAN CIKIN SHEKARAR 1942 WATAN NUWAMBA JAMUS TA MAMAYE KUDANCIN FARANSA DOMIN SU KAMA JIRAGEN RUWANSU SAI DAI FARANSA TA KONA DOMIN KADA YA KOMA ABOKAN GABA.
SANNAN CIKIN SHEKARAR 1934 WATAN AFRILU BARITANIYA TA YAUDARI JAMUS YAU DARAR DA TA BADA MAMAKI TA YANDA SUKA SANYA TAKARDA MAI NUNA CEWA ZASU YAKI WURARE GUDA BIYU A GIRKA, SANNAN SUKA YASAR A GEFAN TEKUN ANDALUS TAYANDA JAMUS ZASU TSUNTA AMMA SU SUNA SONE SUKAI HARI SICILY DOMIN KADA JAMUS SU FAR MUSU DON HAKA JAMUS TAKAI RUNDUNARTA GIRKAS SU KUMA SUN YAKI SICILY .
S HEKARA 1944 WATAN YULI HITILA YAYI ZAMA DA JIGA JIGAN HUKUMARSA DAN GANEDA YAKIN DA SUKEYI KO DAYA SUNKUYA DOMIN YA DUBA TASWIRA SAI WANI BOMB YA FASHE WANDA MUTUN HUDU SUKA RASU SHE KUMA TA SAMI RAUNUKA WANNAN HARI MUTANEN HITILANE SUKA SHIRYASHI DOMIN YANA SASU CIKIN HALKAKA
CIKIN SHEKARAR 1945 RANAR 29 GA WATAN AFRIILU HITILA YAYI WASIYYAR KARSHE WACCE YA MUZANTA YAHUDAWA,SANNAN A WATANNE RUNDUNAR HITILA TA MIKA WUYA GA RUNDUNAR BARITANIYA A ITALIYA, SANNAN WASHE GARI WANI SOJA YA DAGA TUTAR SABIYAWA KAN WANI BENE DA BAIDA NISA DAGA GIDAN HITILA BAYAN HAKA DA KADAN SAI MUTANENSA SUKA JI WANI SAUTI YAFITO DA KARFI DAGA BAKINS ALAMAT YA HADIYE RANSA YA FADI MATTACE ,
ITA KUWA MATARSA SABODA BAKIN CIKI TA SHA GUBA TA BISHI ,
BAYAN HAKANE JAMUS SUKA MIKA WUYA MATAKI MATAKI,A ITALIYA AWATAN MAYU,DAGA NANNE KASASHEN TURAI SUKA KU BUTA DAGA HATSARIN HITILA AMMA SUNYI ASARAR RAYUKA DA DUKIYA WANDA BAZU KIDAYU CIKIN SAUKIBA.
NAKU
AUWAL MUHAMMAD ABDUL KADEER
DAN NAJERIYA A BIRNIN OMDURMAN SUDAN

30.9.07

JAN FURE

15.9.07

KA JI KADAN KA JI MAI YAWA


Ka san me ya faru?

Cikin watan da ya gabata a khartoum babban birnin jamhuriyar sudan, ina tafiya a hankali saboda rashin lafiyar da nake ciki zani asibiti, ban muzgunawa kowa ba kuma ba wanda ya muzguna mun face wannan zazzabin daya fallashi lafiyata a bainar jama'a, ina tafe ina dan sake sake ba wani takamamman tunani da nakeyi duka dai kame kame ne , an jima inyi wakar dankwairo an jima can inyi karanta wata aya, ni kuwa kaftani nasa ba jallabiya ba ba kuma hula kaina, hankalin suma ta ya tashi, ban tsammanin za'a rasa gashin bargo da suka kulla abota da gashina wanda da a kasar hausa ne da yara sun min wasan '"ga wani a bu a kan matan sarki" . ban karkare tone tonen tunani na ba sai sai naji tsawa a baya na

" kai ne limamin wancan masallacin ?"

sai na farka a firgice sai naga wani mutum a yankwane, kasusuwa sun baiyana a fuskarsa , gajere , idanunsa sun yi jajazur kamar gauta , gashi ya daka mun harara.

" a'a ni ba liman bane " nace

" to kai me ye? " ya ja gurnani kamar zakin da aka tsokana

sai naga abun sai hauhawa yake , ga shi sai kokarin huruwa yake

" ni dalibin jami'a ne " nace masa

sai ya zaburo kai na yana nuna mun kashedi yana cewa " wai shin ku 'yan najeriyan nan kafun kozo sudan ba musulunci ne ko yaya? kawai kuna zuwa kuna mana cokiburutsu irin na usama ben laden "

na shafa ko zan ji hakurina , ashe ya sace mun , don haka nima na haukace na fara maganganu da ba nutsuwa ciki " ina ruwanka da 'yan najeriya " " me suka ci maka basu biya ba " " me osama ben laden ya maka " .


Kafin in kare zaiyano abunda ke kwakwalwata sai kawai naga ya suri hoge mai girma wai zai mun rotse
sai nai shiru ina kada kai , na laluba kamus din kaina ban sami komai ba sai wasu kalmomi sai nai maza na hadasu nace " ZA-KA-MUTU! "
Ko da yaji haka sai yace " ka kashe ni a kasa ta? , wannan kasar muce mu mukai gwagwarmaya akan ta "
ba shakka ya fesa mun tsoro a zuciya ta, kuma yasa nayi bitar jimlar da na hada , na karanci ma'anar ta a take sai na fahimci cewa ma'anar ta shine in kashe mutum a garinsu " sai nayi wasu yan sunbatu ina ja da baya da yan dabaru , har na samu na gota shi kuma ya haye katangar hubbaren wani shehunsu mai suna HAMDANNIEL kamar kadangare da dutsen a hanunsa, ni kuwa na wuce ina yiwa kaina barka a raina , don kuwa da ba don kariyar Allah ba da ya kara mun kwankwatsar kayi kan zazzabin nan.

To amma abun tambaya shine me yasa wannan mutumi ya shiga rayuwata na 'yan wadannan dakikai?

AMSA shi dai wannan bakauyen yayi tsammanin cewa najeriya duk kiristoci ne saboda yaga shugabanta Obasanjo kiristane kuma dimukoradiya ta kawo shi , sannan galibin yan kwallon najeriya yaga ba sunan musulmai gare su ba, har sun yi tsammanin Jay Jay okocha musulmi ne mune bamu iya fadan yadda sunan yake a larabci ba wato UKASHA, to duk da haka sai yaje yin salla wami masallaci sai ya tarar limamin dalibine dan Najeriya , don haka yake ganin bai dace ace wadanda suka musulunta jiya da daddare sunzo suna limancin wadanda suka gaji musulunci kaka da kakanu ba.

Amma kai meye ra'yinka

sai naji daga gareka

25.8.07

KWADON DABI'AR DAN ADAM DA MABUDINTA

ABUL HASAN ANNADAWY


Auwal Muhammad Abdulkadir
aazarema@yahoo.com
25-8-07m / 11-8-1228
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata masa ba irin sauran masu gyaran da ke zuwa gidaje ta baya ko su sadado ta taga bane , masu yaki da wasu cututtukan zamantakewa da aibubbukan halaye kawai ba , sai ka samu daga cikinsu akwai masu sa’ar gusar da wasu a sassan wasu garuruwa na dan wani lokaci, wani ma ya mutu bai cimma burinsa ba.
To amma shi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata yazo wa gidan gyara ta kofarsa , kuma ya sanya wa kwadon dabi’ar dan’adam mabudinta , wannan kwadon yana dawuyar sha’ani saboda bude shi ya gagari masu sauyi kafun manzanci dama duk wanda yai kokarin bude shi bayan shi ba tare da mabudinsa ba.
Ya kira jama’a zuwa ga imani da Allah shi kadai, da kin gumaka da bauta da kafircewa dagutu, don haka ya mike cikin jama’a yana cewa “ ya ku mutane ! Kuce ba abun bautawa da gaskiya sai Allah ku rabauta ( ku sami rabo) ‘’ ya kuma kira su zuwa ga imani da manzanci
da imani da lahira .
Mahatma ghandi na kasar hindu a rayuwarsa ta siyasa da gwagwarma ya takaita jagorancinsa da gwagwarmayar sa kan ka’idoji biyu ne .
Na farko: wanda shine takensa (ba muzgunawa ba kare kai) yayi kira zuwa ga wannan ka’ida a matsayin addini da falsafa cikin hudubobinsa da makalunsa da kuma jaridunsa. Ya karar da karfinsa kan haka , to da yake hanyar daya dauka ba hanya ce mai zurfi wajen sauyin zuciya ba bata yi wani tasirin azo agani wa mutanen hindu ba , don haka suka hure ta , suka kashe rabin miliyan na musulmi a East Punjab da Delhi a 1947 miladiya, daga karshe shi ghandin aka masa kisan gilla dukda daukaka shi da bauta masa da wasu suke yi.
Na biyu: shine shafe matsalar fifiko tsakanin kabila da kabila , wanda baiyi nasarar kirki ba, wannan yankakken dalili ne cewa manhajin annabawa shine ya mafi kyau wajen gyara da sauyi.
fassara daga littafin (( Rashin da duniya tayi samakon faduwar musulmai)) na malam Hasan Annadawi.

18.8.07

HAUSA FIM: TARBIYAR TSIRACI

HAUSA FIM: TARBIYAR TSIRAICI
AUWAL MUHAMMAD ABDULKADIR

6/8/1428h-19/8/07m

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
Sanannen abune cewa kasashe masu kaffa-kaffa da
addinin su da al'adunsu na kwarai suna kokarin maida
finafinai da wasan kwaikwayo wata kafa ta tattauna matsalar
alumma da tarbiya da bada tunani na gari, sabanin halinda
muke a kasar hausa na karkatar da wannan dama zuwa
gwada kwarewa wajen nuna rashin kunya da da koyawa
manyan gobe munanan dabi'u daga baya kuma sai ace ana
kokarin gyara tarbiya to lallai bamu ba tarbiya har duniya ta
tashi indai yan daba da mata masu cin gashin kansu da
wadanda aka kasa tarbiyarsu suka gudu suka bar tarbiya su
-ne masu tarbiya kai abun dariya da takaici duk da haka
shuwagabanni da wadanda abun ya shafa basu yi yunkurin
hanawa ko kokarin garkatar da akalar fina-finan izuwa koyar
da tarbiyar gaskiya ba . to yanzu abun yakai ga dole kowa ya
ciza yatsa , akwai matukar da takaici ace yar fim ta fito tsirara
har na tsawon dakikai takwas kan gado sannan wani yazo ya
haukanta yayi tsiyar da zaiyi da ita, sannan yayi wani irin
nau'i na wasa da maniyinsa kan cinyarta , kai ! wallahi ,
na'uzu billahi minashshaidanirrajim! wani irin dabbanci kenan?
kuma abun mamaki harda cewa '' a gafarcemu'' amma
wannan yarinya taci sunanta ''HIYANA'' don kuwa ta ha'inci
duk musulmin duniya, ta kuma tona asirin musulmin najeriya.
Duk wani mai zurfin tunani yasan hakan zata faru tunda
kokari suke su kwaikwayi [nigerian film] su kuwa wannan ba
bako bane gunsu, ga wani abunda na taba karantawa jaridar
gaskiya tafi kwabo ''GTK: To, a matsayinki na wadda take fitowa a fina-finan
Hausa da na Turanci, yaya za ki kwatanta bambancin da ke
tsakanin fina-finanmu na Arewa da kuma na Kudanci?
HAUWA MAINA: Ai dai wannan ne ko kuma aka tambaya, za
ku iya fadin bambancin (dariya).
GTK: Amma da yake ke kina cikin harkar ne, ina ganin ke ya
fi cancanta ki yi mana bayani.

HAUWA MAINA: To shi kenan, a gaskiya, ’yan Kudu sun yi
mana fintinkau in dai za a yi maganar gaskiya ce. Amma
Alhamdulillahi mu ma mun fara shiga sahunsu, saboda idan
aka yi la’akari da irin na’urorin da suke amfani da su, to,
yanzu mu ma mun fara samun irin wa]dannan na’urorin. Haka
kuma ’yan wasanmu na Hausa su ma yanzu sun zaburo, suna
kuma kokari sosai. Saboda haka nan ba da jimawa ba za mu
rika hada kafada da kafada da su.''

Hakika abun daya ban mamaki cikin wannan al'amari babu
kamar wasu masu kokarin wanketa da cewa ai ba fim din
tsiraici bane, saboda wannan wani abu ne tsakaninta da
saurayinta bai da alaka da fim, to amma ai ita jaruma ce a
wannan harka ta tarbiya, wa ya sani ko ta sadaukar da kanta
ne wajen gyara al'adun banza har ta fara yada tarbiya kyauta
ana yada ta a blue tooth cikin kayan mutunci , domin ayi koyi
da ita, sannan an sakar muku haka ne , shin wannan baya
gwada cewa wata ran za'a yi hakan a tsare da furodusa da
dukkan shikashikai da sharuddan fim.

sannan wasu kuma sun bige da cewa taci mutuncin hausa-
fulani ina ruwan wannan matsala da hausa fulani , wasu na
cewa daman ba hausawa bane masu yi , hakika wannan
karya ce mai girma da neman wanke kai na banza da wofi ,
to kai in ma haka ne , waya basu izinin shigowa kano, jama'a
kar mu rudi kammu, hausa fulani dai a duniya zamu bar shi
ba wani abu mai anfani gun Allah sai musulunci.

IYAYE : sune kashin bayan tarbiyar 'ya'ya kuma sune
matakin da idan yaro ya rasa ko sukai sakaci dashi rayuwarsa
zata shiga wani yanayi wanda bara aji dadin karshenta ba,
wani yana cewa '' uwa makaranta ce idan ka shirya ta kamar
ka shirya al'umma ne'' kuma kamar yadda kowa ya sani
wadannan masu cin abinci da lalata tarbiyar manyan gobe
galibinsu in bamu ce duka ba sun fuskanci matsala da iyaye
kamar auren dole ko rashin mai riko mai kyau ko rashin tsawa
da kwaba don haka dole iyaye su dau hakurin daukan kaso
mai girma na laifi saboda kaso mai girman ba suke dashi
wajen jibintan yayansu da kuma damar tarbiya.

YAN WASA: saboda sune masu fuskantar da wannan
matsala zuwa ga alumma kai tsaye don haka duk da barrantar
da kan- su da wasu uzurori da suke bayarwa wanda zai yi
wuya su kansu su yarda da su a cikin zukatansu balle
al'umma gaba daya. Su dai kokarin su dole sai sun kwaikwayi turawa alhali kuwa
kowa yana kokarin bada gudumawane daidai al'ummarsa,
idan bature da baturiya sukai wani rashin kunya a wasan
kwaikwayo to saiku duba cewa to shin kowa a cikin jama'arku
ba rike ya ke da addini ba ? ba tare yake da mafadi ba? Shin
burgewa a garemu shine mu fita daga shingen iyaye da
sunan yanci? Wadannan banbance-banbance na addini da
al'ada idan ba'a duba su ba to zamu jima cikin wannan rami,
mu fito mun yi kura duk wanda ya kallemu ba zai iya
maimaitawa ba.

SHUGABANNI: wato duk Wanda yake da damar fada aji
amma bai hango matsalar da zata iya jawowa masu
zuwa ba, ko ya hango baiyi kokarin kawo sauyi ba .

Daga karshe ina kara rokon wanda abun ya shafa da suyi
hattara wajen daidaita wannan wasa inda zaiyi daidai da
addinin jama'arsu da al'adunsu na kwarai , inba haka ba muyi batan bakatantan bamu ga namu bamu ga nasu .

Allah ya raba mu da sharrin shaidan.

11.8.07

SHURE SHURE BAYA HANA MUTUWA

SHURE SHURE BAYA HANA MUTUWA
AUWAL MUHAMMAD ABDULKADIR
aazarema@yahoo.com
Da yawa mun rudu da sanimmu ko bada sanimmu ba kan abunda amurka da yammacin duniya ke farfaganda kai, na yanci, hakkin bil'adama ,sakulanci (secularism), yakan wariya , girmama addinindan adam ko da ya yake, da sauransu . muna kuma ganin cewa wannan wani cigaba ne sakamakon kokarinsu na amfanar da halittu wanda ba'a sansu ba a baya , wanda kuwa duk wadannan addinin musulunci ya baiyana na kwaransu sannan yayi kafar angulu da wofi daga ciki da isassun dalilai na nassi (kurani da hadisi) ko na hankali .
Alkurani ya tabbatar mana cewa manzon Allah[tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi] rahama ne ga dukkanin halittu , sannan musulunci shine ya sauya alummar larabawa da ke cikin mummunan yanayi na zamantakewa da siyasa da dukkan sassan rayuwa, ibnu abbas yana cewa: “idan kana so kaga yanda jahilcin larabawa ya kai sai ka karanta fadin Allah madaukakin sarki: “ Lalle ne wadanda suka kashe diyansu , saboda wauta bada ilimi ba sunyi hasara ! kuma suka haramta abinda Allah ya azurtasu bisa kirkira karya ga Allah lalle ne sun bace basu kasance shiryaiyu ba ” .[6:140].
Bayani kan sauyin da musulunci ya kawo ba boyaiye bane saidai abunda ya shige mana duhu musulmanmu da kafiranmu shine shin musulunci yazo da abubuwanda yammaci ke takama dasu koko? Kamar yadda muka yi bayani a baya ya tabbatar da wasu, ya kuma sa wasu a gefe.
Zamu iya ganin yadda musulunci ya kimata dan adam cikin fadin Allah madaukakin sarki: “ kuma lalle mun girmama 'yan adam , kuma muka dauke su a cikin kasa da teku , kuma muka azurtasu daga abubuwa masu dadi , kuma muka fifitasu a kan da yawa daga wadanda muka halitta, fifitawa ” [ 17 :70] .
Manzon Allah [tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi] da aka tambayeshi hakkin mace gun mijinta sai yace “ ka ciyar da ita idan kaci , kuma ka tufatar da ita idan ka tufata , kuma kar ka bugeta a fuska , kada kuma ci mutuncinta , kar kuma ka kaurace mata saidai a cikin gida” wannan hadisi an samo shi ne kafin wani abu da ake cewa (CEDAW) . Musulunci har wayau ya tabbatar da kulawa da tausayawa yara kamar yadda yazo cikin hadisi cewa wani bakauye yaga manzon Allah[tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi] ya sunbanci yaro sai yayi mamaki yace shi yana da yara goma amma bai taba sunbantar ko daya ba , sai abun yayi nauyi wa manzon Allah tsira da aminci sutabbata a gareshi har yace: “ to ya zanyi idan Allah ya zare rahama a zuciyarku¡?”.
Musulunci bai ba wariya kafar shiga ba Allah yana cewa “yaku mutane lalle ne mun halittaku daga na miji da mace , kuma muka sanyaku dangogi da kabiloli domin kusan juna”.[49:13]. Kuma cikin hadisi Abu zarri Allah ya yarda shi ya bada labari cewa ya samu sabani da wani danuwansa wanda mahaifiyarsa ba'ajamiya ce ( ba balarabiya ba) sai ya aibace shi da mahaifiyarsa , da labari ya isa wa annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi sai yace: ya kai abu zarri, lallai akwai jahiliya a tare da kai, su 'yan'uwanku ne Allah ya sanya su a cikin hannun ku , don haka ku ciyar dasu daga abunda kuke ci ,kuma ku tufatar dasu daga abunda kuke tufata dashi , kuma kar ku daura musu nauyin da baza su iyaba, idan kuma kun daura musu to ku taimake su,” kamar yadda Allah ya nuna cewa tsoronsa kawai shine fifiko tsakanin jama'a kan wasu sabanin yahudawa masu riya cewa sune zababbun agun Allah [ God’s favoured nation] , kuma sune masu gudanar da tsarin mulkinsu kan tatsuniyoyin da suke samowa daga Attaurar da hannu yayi wasa ciki , kenan su basa raba addini da siyasa amma duk da haka tana samun kariya daga amurka da sauran manyan kasashe , kai har shi kansa BUSH ya kasa aiki da tsarin “ na sarki na fada , na Allah na masallaci” ko “[ Give unto God’s , what a God’s, and unto Caesar what a Caesar;s] tun da an tambayeshi wanene babban malamin falsafa a siyasar sa sai ya kada baki yace : yesu almasihu”. Girmama addinnai kuwa ma'anarsa a musulunci ba shine jin cewa wani addini koma bayan musulunci shine gaskiya ba , innama ma'anarsa zama da kafirai ba tare da tsangwama ba idan an yi alkawarin lumana dasu , Annabi kuwa yayi zaman alkawarida da yahudawa a madina dukda cewa daidaikunsu suna kokarin kashe shi kamar yadda wata bayahudiya ta sa masa guba cikin abinci , kuma sunyi kokarin jefo masa dutsen markade daga kan bene , amma duk da haka bai far musu ba saida suka saba alkawari a fili da suka hada kai da mutanen makkah wajen yakarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi. Wannan shine yasha banban da abunda masu kirayen-kirayen sukeyi na tuhuma addini daya cikin dubban addinan duniya da taaddanci , ko jifa da littafin addini daya cikin kazanta , ko siffanta manzon wani addini daya da harijanci da ta'addanci, duk wannan suna yine domin kara kwanakin daularsu , amma kuwa akasin haka ne ke faruwa don kuwa duk sanda suka kunna wata wuta kan musulunci sai samarukansu sun bi diddigi sun fahimci karyansu kuma sakamakon haka su shiga musulunci jama'a- jama'a , Allah ta'alah yana cewa :[ lalle ne wadanda suka kafirta suna ciyarda dukiyoyinsu, domin su tare hanyar Allah , to zasu ciyar da ita ,sa'annan ta kasance nadama a kansu , sa’annan kuma a rinjayesu”, [8:36], kuma yana cewa “ lalle ne , wadanda suka zo da karya wadansu jama'a ne daga cikinku , kada kuyi tsammanin hakan sharri ne a gare ku, a'a alheri ne a gare ku”. [24:11].

Reality

There are many wide spread ideas among westernersprophet Muhammad peace be upon to him , Qoran and islam in general.
Accoding to conservertives ''prophet Muhammad's life is bloody , his teaching is vicious ,and he is founder of the world most intolerancAe religion (islam).
such kind of un objective accusation awake there peaple for searching truth and reality about prophet Muhammad not from his enemy but from what has been sent down to him , and his wisdom .