6.1.08

BENAZIR BHUTO DA GUNKIN DABINO


Bilawal Bhutto dauke da hoton marigayiyar


Sau da dama wannan zamani yana kawo wasu wakoki da ake rerawa da har yanzu wasu wanda ni ma Alkalami ina daga cikinsu mun kasa gane hakikanin ma'anarsu , mu samman wakar nan ta Dimukuradiya wanda na hakikance cewa kidine kawai akeyi ake rausayawa , amma ba wata kalma ko jumla ciki bare a fahinci manufarta.

ku yafeni ya ku mabuga tamburan dimukuradiya in abun bai muku dadi ba , amma yadda ya wajaba in nunfasa haka kuma ya wajaba in baiyana irin wannan rainin hankalin da nake ji a cikin kade kaden dimukuradiya .

Allah yayi cikawa wa malama Benazir Bhutto tsohuwar firayim minista kuma 'ya ga tsohon firayim minista Zulfikar Ali Bhutto wanda ita da mahaifinnanta duk mabiya tafarkin shi'a ne , a yanzu dai ana kokarin ganin binciko wadanda suka yi wannan buruntu, inda shugaba Pervez Musharraf ya daura alhakin wannan kisan gillan ga Alka'ida saboda ita bhutto ta sha lasan takobin murkushe an alka'idan , sannan kuma suna ganin itace takeda cikakken goyon bayan amurka da yan barandanta fiye da kowa a pakistan saboda shi musharraf namiji ne kuma soja don haka akan samu tangarda dashi , baya bi a makance , sannan a bangare guda kuma za'a iya tuhumar shi musharraf din saboda jagorancin da take yi na kokarin kadashi a zabe mai zuwa.

Abunda ya ja hankalina kan wannan waki'a shine yanda dimukradiya ta dawo gunkin da akayi shi da dabino , in aka koshi ayi masa sujjada in kuma aka ji yunwa a ringa gutsura anaci , ta inda ita bhutto ta bar wasiyar a daura danta Bilawal Bhutto dan shekara 19 wanda yake karatun tarihi a jami'ar Oxford kan karagar jam'iyar Parkistan People Party { PPP} , wanda shine kenan zai fito takara da Musharraf , shi kuma mahaifinsa Asif Ali Zardar mataimakinsa. haka nan shugaba Gaddafi {dukda cewa shi ba kan tsarin dimukuradiya yake ba , amma jamhuriya ne ba mulukiya ba} yana neman daura dansa Saiful-islam kan mulki bayansa , haka ma shugaban masar mubarak nufinsa kenan, marigayi Hafez Asad shima ya daura dansa Basshar Al-asad a Syria .

Abun mamaki jaridar Almizan dangane mulukiyar Benazir Bhutto cewa tayi :

''
A yayin da kasashen duniya ke ta kiraye-kirayen a samar da wani kwamitin bincike na kasa-kasa da zai binciki masu hannu a harin da aka yi wa Bhutto, tuni har jam’iyyarta ta zabi danta da mijinta a matsayin wadanda za su ci gaba da jan ragamar jam’iyyar don fuskanta zaben da ke tafe ''.
zaka iya karanta wannan rahoto nasu a yanar gizo ta wannan adreshi http://www.almizan.net/bls803c.html, alhali kuwa shafin yanar gizo na malama Bhutto ya tabbatar cewa gadar wa danta da mahaifinsa tayi in da ya baiyana cewa :

'' Benazir Bhutto's 19-year old son has been appointed chairman of his late mother's opposition political party in Pakistan.

Bilawal Bhutto, who is reading history at Oxford, will chair the Pakistan People's Party with his father, Asif Ali Zardar, as co-chairman.

Bilawal Bhutto right, being comforted by his father Asif Ali Zardar. Party officials made the announcement after the reading of Miss Bhutto's will following her assassination last week.'' , za kuma a sami wannan a cikin shafinta mai adreshin http://www.benazirbhutto.co.uk/Default.php

to abun tambaya ko me yasa yan shi'an basa so ace gadarwa tayi , Allahu a'alamu!


wannan na nuna cewa yanzu ma'anar dimukuradiya ya tashi daga hukumar jama'a zuwa hukumar gado kuma koda magajin karami ne dan shekara shata tara .

wannan bazai bada mamaki sosai ba idan muka tuna cewa Amurka su suka fara taya Moi Kibaki murnar komawa kan mulki dukda sun san cewa bashi ya lashe zabenba , amma tunda sunsan ba dole ne Odinga ya sake musu kamar yadda kibaki yabari suka ringa diban musulmai suna kaiwa Gwantanamo ba da sunan ta'addanci, sannan baza mu mance cewa Hamaz suka ci zaben palasdinu ba, amma turai gaba daya suka juya musu baya suka ringa azabtar da jama'ar da yunwa saboda basu zabi wadanda su { turai } suke so ba wato Fatah .
Allah yayi gaskiya da yace '' yahudu da Nasara basu yarda da kaiba harsai kabi tafarkinsu ''



2 comments:

Anonymous said...

May I simply say what a relief to find a person that really understands what they are discussing over the internet.
You certainly know how to bring an issue to light and make it important.
More people really need to check this out and understand
this side of the story. It's surprising you are not more popular because you most certainly have the gift.

My homepage ... landhausmode crailsheim

Anonymous said...

buy electronic cigarette, electronic cigarette brands, smokeless cigarettes, e cigarette, electronic cigarette, best e cigarette