23.5.10

munafuncin aku


A makonni kadan da suka gabata ne yan Najeriya kowa ke tofa albarkacin bakinsa kan wani ango da wata amaryar da aurensu yafi kowane aure shahara a Najeriya. Wannan angon ba wani bane face Ahmad Sani yariman Bakura wanda ya shekara takwas a matsayin gwamnan jihar zamfara , sannan a halin yanzu yake matsayin sanata mai wakilcin daya daga bangarorin jihar . Lokacin mulkinsa Ahmad sani ya zama zancen daukacin mutanen Najeriya daga addinai , bangarori da harsuna daban-daban wasu na yaba masa wasu kuwa na kushe shi kan yunkurin da yayi na tabbatar da shari’ar musulunci a jihar da Allah ya bashi riko , wanda yanzu haka gwamna yana matsayin sanata sakamakon zaben daya lashe ba tare da wani magudi ba.

Babban tabon da wannan gwamna yake dashi a wajen kasashen waje da wasu kungiyoyi masu riya kare hakkin dan adam da wasu masu riya fafutukar Islama shine kokarin dawo da martabar dokokin Allah, saboda gaba da addinin , wasu kuma saboda ba jagoransu bane ya samu nasarar hakan . wani na kusa dashi Malam Ibrahim Wakkala a wata laccar daya mana ya sanar damu cewa a kasar Ghana wasu mutane sun masa alkawarin makudan dalolin Amurka don ya janye wannan niya tasa amma hakar su bata cimma ruwa ba .

Daga cikin nasarorin da wannan mutum yaci shine ya sanar da mutanen kudancin Najeriya me ake nufi da kalmar Shari’a wanda kafin hakan basu santa ba , sannan ya kara kaimi wa kotunan shariar musulunci don kada suyi kasa a gwuiwa wajen zartas da hukuncin Allah koda kuwa yanke hanu ne ko jefewa , hakan ya yunkurar da jama’ar sauran jihohi har suka tursasa gwamnoninsu zartarwa ala tilas.

Idan muka ajeye son zuciya da son shahara zamuga cewa shari’ar musulunci wani kwas ne wanda ake karantarwa a jamio’in kasar nan sannan aka ba lauyoyi damar kafa hujja da tanadinsa a gaban alkali, to meye laifi don wani yayi kokarin tuka shi gaba? Toyau Allah ya kawomu wata rana wanda abokan gaban yarima suke ganin cewa zasu rama tabbatar da shari’ar da yayi .

Bari in gaya wa mai karatu cewa wadannan kungiyoyin kare hakkin dan adam , mata da kananun yara akwai munafunci cikin aikinsu tunda basu taba zuwa gidan karuwai don su kama matan dake kasa da shekara sha takwas 18 sun dauki wani mataki a kansu ba , sai kawai don sanata yarima ya auri mace aure na sunna ,ba zina ba , ba kuma fyade ba da sadaki a kuma babbban masallacin Najeriya a gwamnatance suna ta daga jijiyar wuya suna kashe tituna. Wani abun ban dariya abun Hajiya Ramatu Bala Usuman taji kunyarsa shine wannan amarya bata ce muku bata son angonta ba , ba kuji labarin cewa auren dole ala mata ba , kuma baku san takaimaiman shekarunta ba , wata kila baku san sunanta ko kunga hotontaba , kawai a jita-jita kun tada zanga-zanga don aiki bai ishe kuba .

Zan so in waiwayi makalar wani marubuci Mahmoon Ahmad Baba mai taken AKAN BAR HALAS DON KUNYA wanda ya rika kiran wannan amarya YAR KWAILA , amma ba mamaki bai sani bane , amma a matsayina na wanda yaje kasar masar har sau uku kuma yasan irin girman larabawa zan tabbatar maka cewa balarabiya yar shekara sha uku zata zuba da yar shekara ashirin da uku a gummu ko ma fiye .

Ban ji labarin wadannan kungioyi sunyi wata zanga-zanga ba sanda akai wa malam jafar kisan gilla , in sun ce su masu kare hakkin dan adam ne , to shi malam kiyashi ne ? in kuma masu kare hakkin mata ne , to ko shi baida mata ne ? ko sanadiyar rashinsa rayuwarta baza ta gurgunta ba ? , in masu kare hakkin yara ne , to shima ai yana da yara , ko ba irin wadannan yaran ake karewa ba ? abunda ya baiyana shine wadannan kungiyoyi ana amfani dasu ne daga kasashen waje don tozarta musulunci da bakanta shi , basu da wani abun cewa sai wanda aka sasu suce kamar aku kuturu , shi yasa nake tare da Ado sale kankiya inda yake cewa ‘‘ abunda na fahimta daga kwakwazon kungiyoyi shine kasashen turai dana Amurka dana yahudawa da suka sa addinin musulunci a gaba ne kawai suke amfani dasu domin su cimma burinsu na rusa addinin Islama da musulunci ’’

Duk wani bita da kulli baza a iya mancewa da yarima ba a bangaren ciyar da Shari’ar musulunci gaba ba , don kuwa duk sanda aka fara da shehu usumanu Dan hodiyo za’a yi ta gangarowa har sai an fadi akan Ahmad sani , kafin wani mujaddadadin ya biyo baya .

Allah ya rabamu sharrin masharranta



Auwal Muhammad Abdulkadir
alkalami1@yahoo.com
+2347030703318
Bauchi
www.alkalami.blogspot.com