8.6.08

Ya zamuyi turai su somu?



Shugaban kasar faransa ya jaddada kinsa kan bawa kasar turkiya mambanci a kungiyar taraiyar turai , saboda kasancewarta kasar musulunci.

A da can shugaba Sarkozy yana fakewa ne da cewa turkiya ta sabawa kasashen turai a al'adu da kuma jogiranfance , don haka ba dama ta samu shiga taraiyar turai saboda kar a ringa samun karo , Amma hira da 'yan jarida sukai da shi a ziyarar da yakai kasar Poland ya fito sarari ya baiyana cewa bazai iya yarda da kasar da mafiyawancinta musulmai ne su samu kujera a taraiyar turai ba , koda kuwa sunbi tsarin Ba'addini (sercularism) .

Wannan bayani zai iya baiyana irin kiyaiya da Sarkozy da sauran kasashen turai suke wa islama da kuma fargabar yaduwansa a cikin al'umarsu , sannan hakan ya kaisu ga kokarin kashe musulmai don kokarin rage adadinsu a duniya musammam in muka dubi karfin soji da Amurka ke kashe Iraki da Afgahnistan dashi , da durawa wa yara 500 kwayoyin cutar Aids a kasar libiya da majinyatar kasar Bulgeriya sukayi wanda shi Sarkozy da matarsa da ya rabu da ita Cicilia sarkozy sukayi ta fadi tashi saida shugabn Libiya ya sake su da sharadin za'a hukuntasu da dokokin kasarsu , amma koda suka sauka a filin jirgin kasarsu sai hukumar kasarsu ta sanar da cewa ta musu afuwa .


Idan muka waiwayi tarihi zamu fahimci cewa birnin Istanbul ko kusdandiniya (constantinople) shine ya mulki duniyar musulunci bayan daular Umawiya da daular Abbasiya tun 1290 karni na 13 miladiya har zuwa 1923 sanda Mustapha kamal Ataturk yai kutunguilar rusheta .

Wannan kangararren mutumin ya shahara wajen kin musulunci da kawazucin al'adun turai , har an rawaito yana cewa " ya wajaba mu tattari daukacin Al'adun turawa kyawawansu da munanansu harda tsutsotsin tumbunansa" don haka ya hana kiran salla da yaren larabci , ya kuma hana gaisuwa da lafazin " Assalamu Alaikum " saidai a sha hanu a wuce , sannan ya haramta auren sama da mace daya , da sanya hijabi , ya musanya kalandar Hijiriya da ta miladiya, ya musanya hutun mako zuwa lahadi maimakon juma'a , sannan ya musanya dokokin shariar musulunci da daular usumaniya ta ke bi da dokokin kasar Switzerland (Swiss civil law) 1926 , duk don ya samu karbuwa ga turawa , da alama bai taba karanta ko jin fadin Allah ta'ala " yahudu da Nasara baza su yarda dakai ba sai ka bi tafarkinsu " kamar yanda Suhgaba Sarkozy ya tabbatar da hakan.


Naku Alkalami

4.6.08

Malam Isa da Alhaji Mu'azu



Ba shakka tunda aka fito da wannan sabuwar siyasa ko ince tun 1999 Malam isa yuguda ne yayi gwamna a jihar Bauci da zabe mai tsarki , don kuwa zaben farko tsakani PDP da APP ba Ahmad Mu'azu ne ya lashe ba , baba Ajiya ne yayi kaye ( kan wuka mai wuyan kamu) amma tsagera suka masa rashin kunya , sannan lokacin ta zarce ma baici ba saboda kowa na bukatar masara ida a rufe don haka masara sak ! ake yi . Amma da tura ta kai bango lokacinda jama'a suka fahimci cewa wannan mu'azun dan rainin wayo ne , suka fito kwansu da kwarkwatansu don su hana shi sanata su hana dan gaban goshinsa Nadada umar gwamna , suka sadaukar da kansu suka don kwato yancinsu daga mahandama , suka tabbadar hikimar Hausawa mai cewa " Sarkin yawa yafi sarkin karfi " .
sau da dama yayin da za'a zalunci mutanen bauci , da sunyi wani dan kokarin kwato hakkinsu sai wani mai anguwa ko yaje gidan rediyo yace wai an san Bauci da zaman lafiya , tun sanda Shehu usumanu ya musu addu'a " . ko me yasa jama'ar Bauci suka yasar da irin wadannan sakarkaru maganganu? , ina ganin wuce irin azaba suka sha a zamanin Amadu mu'azu.
A zamanin Amadu a tunanina babu wani abun da yayi wanda ya ja hankalina kuma na jinjina masa kamar kokarin da yayi na taimakawa musulman pilato , fara daga rigimar addini na 11 ga watan satumban 2001 har izuwa rikicin yalwan shendam , ba shakka wannan abun azo a gani ne.

Wani abunda kuma zamu iya fahimta harwayau shine duk irin badakalar da aka shirya a zamanin PDP a jihar Bauci yuguda yana da kaso a ciki ,yayi shekara takwas cikin jam'iyar hasalima za'a iya fahimtar cewa gogaiya suke da Amadu mu'azu kan jagorancin jihar , don koda sabanin da ke tsakaninsu ya baiyana a sarari har gamagarin jam'iya suka fahimta sai ya baiyana cewa daman don Isa yuguda suke jam'iyar ba don mu'azu ba , wannan kuwa baya rasa nasaba da irin sake hanu da facaka da ya kware kai, sannan ba wanda ya isa ya wanke Isa dangane da irin murdiyar zaben 2003 wanda shi yaki a masa 2007 ,
ah ashe ba dadi ?!

wata tsaka mai muya da malam Isa ke fuskanta ita ce matsalar 'Yan -sara -suka duk da cewa sun dasu kuma suka ciro a mukumar Alhaji mu'azu to amma a hukumar malam Isa sun riga , sara da sassaka baya hana su toho .

Amma ko ba komi kamar yadda malam Abubakar gero ke cewa " Da bakikkirin gwara baki-baki "

Naku Alkalami.

Sawun giwa ne ya taka na rakumi !

Cikin lokacin da nauki tsawon lokaci ban ba blog abinci ba , nakan leka blogs din yan'uwa inga wasu maudu'ai da ya kamata ince wani abu akai , amma yanayi irin na jarrabawa bazai banni in rubuta koda wata karamar makala ba , amma yanzu Allah ya kadara mun kammala jarrabawa , giwa ta daga sawunta daga kan na rakumi

Naku Alkalami