9.8.08

Rayuwar da Alkalami bazai manta ba


Ya salam ! , komi yai farko zaiyi karshe , shekara kuma kwana ne , kamar kwana hudu da suka gabata na sauka a filin jirgin Khartoum da Abokan karatuna kamar karfe 9:00 pm , lokacinda aka fito damu zuwa masaukinmu ba abunda nake kokari sai in kalli yanayin farkon kasar da na fara shiga ba tare da na kyafta ido ba , musamman sanda muka hau gadar da ke kan Nilu in da na hangi wani dan karamin tsibiri a ciki , haka dai cikin kallace-kallacen gari da masu garin , muka isa masaukinmu , wasu fuskokinda dama munsansu suka taryemu da sowa , wadanda suka fara ganinmu a ranar kuma suka mana barka da zuwa kowa yaje kashe wutar gabansa .
Ni dai fatata da tsikar jikina tana isar mun da sakon bakunta , da kewar gida Najeriya .

Wani gari da waye , dan uwa Bashir ya tattaremu muka je wani abu mai kamada rangadi a Jami’ar musulunci ta Omdurman (Omdurman Islamic University ) wacca itace aka bamu gurbin karatu a ciki , dama dai ina da karamin sani dan gane da Jami’ar , saboda kanen kakana Ambasada Abba Abdulkadir samada shekara 30 shima nan yayi karatu , wata ran kuwa da akayi sharan dakin littafansa , an bani wasu littafansa daga ciki harda Dalilin( brochure) tsangayar osuluddin , a matsayina na dalibin Arabiya .

Mun fara karatun A jamiar inda na shiga tsangayar shari’a and law , muna tattaki wani lokacin yayi saibi kamar tafiyar hawainiya wani kuwa muga kyaftawa da bisimillah ya gilma kamar walkiya , wata rayuwar tai mini zaki kamar zuma wata tai mun daci kamar shuwaka , wata kuwa tamun tsami kamar tsamiya , tsada ko lemon tsami .
Mun shiga fargaba daban daban kamar mutuwan mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan tawaye daya fadi a jirgi bayan kwana Ashirin da bashi mataimakin shugaban kasa , cikin birnin Khartoum ya dauki dumi don kuwa wasu sun rasa rayukansu wasu sun rasa dukiyoyinsu wasu matan kuwa sun rasa mutuncinsu sakamakon fyade da mutanen mamacin sukayi da hujjar cewa hukuma ce tai kutunguilar kashe shi , ni dai ban rasa komi ba sai aminci da tsoro ya koreshi , sai kuma hawaye saboda wata motar kabokabo da aka kona a kofar gidanmu , hayakinta ya ringa tultula gidanmu .

Abunda yafi tada hankalina babu kamar rashin lafiya da nayi a karshen shekara ta uku wata biyu ana mun allura ina kuma hadiyar kwayoyi takwas, sauran wata shida kuma ina shan kwayoyi bibiyu duk wayewar gari . wannan mawuyacin yanayi da jikina ya shiga ya kama hanun zuciyata sun tafi don kuwa har nayi shawarar jingine karatun zuwa shekara mai zuwa in dawo gida don jinya ,
Cikin wannan rashin lafiyar kuwa Allah ya jarrabeni da yan sudan don kuwa farko-farkon ciwon wataran na kama hanya zuwa asibiti ina tattaki ina karatu wani sa’in ina wata yar waka da zata sanyaya mun zuciya ita kuma ta sanyaya mun jikina , ni kuwa kaftani nasa ba jallabiya ba, ba kuma hula kaina, hankalin suma ta ya tashi, ban tsammanin za'a rasa gashin bargo da suka kulla abota da gashina wanda da a kasar hausa ne da yara sun min wasan '"ga wani a bu a kan matan sarki" . ban karkare tone tonen tunani na ba sai sai naji tsawa a baya na

" kai ne limamin wancan masallacin ?"

sai na farga a firgice naga wani mutum a yankwane, kasusuwa sun baiyana a fuskarsa , gajere , idanunsa sun yi jajazur kamar gauta , gashi ya daka mun harara. Ya kuma nuna wani masallaci , wanda ni banda wata alakata dashi data wuce cewa wani lokaci na kanzo karatu ciki ba , anan ne kuwa na taba ganin tsohon shuguba Sadiq al-Mahdi yazo daurin aure .

" a'a ni ba liman bane " nace

" to kai me ye? " ya ja gurrnani kamar zakin da aka tsokana

sai naga abun sai hauhawa yake , ga shi sai kokarin huruwa yake

" ni dalibin jami'a ne " nace masa

sai ya zaburo kai na yana nuna mun kashedi yana cewa " wai shin ku 'yan najeriyan nan kafun kozo sudan ba musulunci ne ko yaya?

na shafa ko zan ji hakurina , ashe ya sace mun , don haka nima na haukace na fara maganganu da ba nutsuwa ciki " ina ruwanka da 'yan najeriya " " me suka ci maka basu biya ba " .


Kafin in kare zaiyano abunda ke kwakwalwata sai kawai naga ya suri hoge mai girma wai zai mun rotse
sai nai shiru ina kada kai , na laluba kamus din kaina ban sami komai ba sai wasu kalmomi sai nai maza na hadasu nace " ZA-KA-MUTU! "
Ko da yaji haka sai yace " ka kashe ni a kasa ta? , wannan kasar muce mu mukai gwagwarmaya akan ta "
ba shakka ya fesa mun tsoro a zuciya ta, kuma yasa nayi bitar jimlar da na hada , na karanci ma'anar ta a take sai na fahimci cewa ma'anar ta shine in kashe mutum a garinsu " dukda cewa dai dama barazana ce ,sai nayi wasu yan sunbatu ina ja da baya da yan dabaru , har na samu na gota shi kuma ya haye katangar hubbaren wani shehunsu mai suna HAMDANNIEL kamar kadangare da dutsen a hanunsa, ni kuwa na wuce ina yiwa kaina barka a raina , don kuwa da ba don kariyar Allah ba da ya kara mun kwankwatsar kayi kan zazzabin nan.

To amma abun tambaya shine me yasa wannan mutumi ya shiga rayuwata na 'yan wadannan dakikai?

AMSA shi dai wannan bakauyen yayi tsammanin cewa najeriya duk kiristoci ne saboda yaga shugabanta Obasanjo kirista ne kuma dimukoradiya ta kawo shi , sannan galibin yan kwallon najeriya yaga ba sunan musulmai gare su ba, har sun yi tsammanin Jay Jay okocha musulmi ne mune bamu iya fadan yadda sunan yake a larabci ba wato UKASHA, to duk da haka sai yaje yin salla wami masallaci sai ya tarar limamin dalibine dan Najeriya , don haka yake ganin bai dace ace wadanda suka musulunta jiya da daddare sunzo suna limancin wadanda suka gaji musulunci kaka da kakanu ba.

Amma kai meye ra'yinka

sai naji daga gareka
Bayan kwana biyu ko kasa da haka ko sama da haka wani abunda da yafi takaici gareni ya faru , shima na fito zani Asibiti ban san sami mota da wuri ba , sai daga karshe motar da na samu ta cika sai a tsaye na tsaya banyi auni ba sai naji naushi koda na juyo sai kowa yak au da kai , sai kawai wani baba dake bani hakuri , koda na kuma juya wa sai na kuma ji wani naushin sabo , na juyo cikin fushi da radadin rashin lafiya , sai babannan ya kara bani hakuri , duk wadannan naushe-naushe ban san mai yinsu ba kuma ban san daliliba , sai daga karshe naji wai sanda nake tsaye na taka wani dan kudancin garin kuma da alama cikin maye yake , amma abun mamaki koda nayi martani cikin fushi sai na zama mai laifi , mata da maza na mota sukace dama mu baki mune muke kawo rigingimu cikin sudan , muryoyi daban daban wata a baiyane wata a dashe kowa yana mun tofin Alatsine , koda naga abun ya kasa hawa mizanin adalci saina dakatarda Karen mota nace ya sauke ni na kara da addu’a a baiyane kowa a motar saida yaji nace “ Allah ka fitar damu daga garin azzalumai ” .

Wadannan ababa da suka faru dani har suka sani cikin damuwa wani abune dake gwada cewa rayuwa launin fari ne wata ran kuma baki wataran kasha zuma ,wataran kuwa kasha madi , wataran kasha madaci ,don kuwa zaiyi wuya mutum ya sami mutumin kirki a doron kasa kamar dan sudan mai girmama kowa da rashin girman kai , mutane duka daya ne maikudi da talaka , koda kuwa shugaban kasa ne , yana daga abunda muka ji labari daga wadanda suka rigayemu cewa sanda akai wuyar man fetur a kasar shugaban kasa in ya fito yakan debi yan kasa ya rage musu hanya , lokacin muna nan kuwa wataran da sudais ya kawo ziyara kasar jama’a kamar tawagar tururuwai kowa na so ya gaisa dashi , koda shugaba yaga an gajiyar da bakonsa sai ya kutso ya tare shi yaba jama’a baya yana hanasu sai suka ture shugaban kasa yai kasa koda yaga abun yafi karfinsa saiya ja gefe , muma almajirai mukan halarci wasu tarukan da shugaban kasa ke zuwa kuma mu zauna a sahun gaba – gaba , ina tuna wata ran da ya shigo taro aka mike ana taken kasa nidai da Habib tijjani da Ibrahim muktar bamu mike ba kuma tsakaninmu da shugabansa baifi sahu hudu mukai ido hudu dashi amma muka ki mike , kuma muka ki mike wa muma mu sandare , Allah ja zamaninka Bashir .

Cikin wannan tattaki daga yini zuwa yini ,mako zuwa mako , wata zuwa wata , shekara zuwa shekara , muka farka muke jin kamar labarin cewa muna shirin jarrabawar fita a jami’a , wannan ya razana zuciyata matuka , musamman inya tuna cewa ya kamata mutun ya karbi sakamakonsa da hanun dama yaje gida yana kadata kamar tuta kowa ya gani , muna cikin jarrabawa “ wataran ina karatun jarrabawa a wani masallaci mai jan fenti a gefen titi , dama dai munji wani abukamar jitajita cewa yan tawaye zasu shigo da niyar juyin mulki , amma duk mun dauka kamar yadda suka saba ne , suce zasu zo amma ba ganin ko kuransa , da haka nidai na dauko littafin Public finance ina karantawa saboda jarabawansa zamuyi jibi , koda na leko ta taga sai naga gare ya sake fuska kamar ba wanda na sani ba sai na fito in ganewa idona koda muka fito sai naga jerin gwanon motocin masu sulke da na take suka fara bude wuta cikin iska , wani yanayi ne wanda ban taba tsammanin zan sami kaina a ciki , a lokacin na san ma’anar tawaye da kokarin juyin mulki , ana ta rowan harsashai masallaci kuma ya zama kamar kasuwa kowa ya fado ciki , maza da mata , musulmi da aljihun baya, kowa wasu na rarrafe wasu na ni kuma ina bayan ginshikin masallaci tsoron kada a harbo wani abu ya fasa gini ya shigo ya mun rauni , kuma ba shakka hakan ta faru amma Allah ya tsare , sudai wadannan yantawaye sun fara jin kanshin gidan shugaban kasa , amma karshe sunyi kicibis da dakarun hukama inda aka ba hammata iska aka taushe su aka kamasu , sai dai abun takaici cikinsu akwai kananun yara yan shekara12 , 13, 14, wasu an kaisu barzahu wasu an kamesu .

Cikin bugawar zukata muka kare wannan jarrabawa amma da ikon Allah sakamakon ya fito na sami matakin na biyu a tsarin darajar sakamako wato Very good wanda yake farawa daga 70 zuwa 79 ,

Na kare rayuwata ta sudan zan barta ina mai tuna ranarta da tasha banban da irin ranar sauran duniya , wacca Allah ya kwararar da Nilu a cikinta manoma suna kwararawa wa gonakinsu dake bakin gaba , makiyaya suna shayarda dabbobinsu , masunta suna kamun kifi , ni kuwa almajiri a ina shan wata iska mai debo danshi zuwa gare ne , ina jin dadin haddan abun day a wajaba in haddace , ina fahimtar abunda ya wajaba in fahimta , ba shakka rayuwa ce mai dadi amma ban san abunda yafi dadi ba shin sanin wani waishi bashir dab sakkwato , wanda ya dauke ni kaninsa yake ban hakuri don inci abinci kamar karamin yaro , wanda ya gama karatunsa ya tafi ya barni kamar maraya , ko haduwa da Mustapha bangon gishiri dan shehu barnoma , ko Habibu tijani da muka karasa rayuwar da muka fara a Jos ko Ibarahim dan baba wanda na sanshi a nan sudan amma kamar tare mukai yaranta , ko yusuf Nabahani comtuper man , ko Awwal bakoshi bangon dutse mai wuyar isa , ko umar hamza maim un ahnun ka mai sanda daga nesa , ba shakka rayuwace mai zaki kuma wucewarta daci ne dauwamamme .

Bazan iya mance kirkin muttanen dakin da nake kaikawo zuwa gareshi ba , sai sani musa ya miko mun magani na in sha , kabiru a bamu wani labarin raha , Naziru ya fadakar dani zubairu miko mun taliyar Indomie , bana fita daga dakin sai sun warkar da jikina da zuciyata , Allah ya bar zumunci.

shin zamu iya fahimtar gaskiya tsakanin shi'a da sunna ta waki'oin siyasa ?

Iran da Amurka fuska biyu ga kobo daya

Dalilin wannan tambaya shine wani rubutu da naga wani bawan Allah yayi yana mai tabbatar da ingancin mazhaban shi’a wanda ya ginu kan zagin sahabbai , da matan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi , da irin gaban dake tsakanin Jamhuriyar Iran , da kasar Amurka , ko artabun da akai tsakanin Hizbullah da Isra’ila .

Sau da dama hakan ake tunani , sai muyi wa mangoro hakunci da bawon da ya lillubeshi , wannan kuwa zai boye mana da dama daga cikin gaskiyar da muke nema , wannan ma ya tunamun wani da yayi shigan wani Akaramakallahu , da babban rawani da duk kayan da jama’a zasu yi tsammanin Shi na kwarai ne , ya sauka wani gida wanda daga karshe ya sace musu yaro yayi gaba .

Ya kamata mu tuna cewa siyasa abace da ke ta’allake da alfanu , kowace kasa ta hangoshi zata garzaya ta kawo wa kanta , ko da daga makiyarta ce , sai tayi mata zakin baki da lallashi , don haka wasu suke ganin siyasa ba makiyi na dindindin ba kuma aboki na dindindin .

Ita dai gaskiya daya ce amma in muka dauki ma’aunin da wannan dan shi’a ke amfani dashi zamu ga gaskiya sun zama barkatai , saboda Amurka bata da abokin gabanda ya wuce Osama ben laden , tunda shine ya kwance mata a kasuwa , ya gwada wa duniya cewa Amurka bata isa tayi aikin Allah Ta’ala ba . kuma har tayi nasarar tabbatar wa Al’umar duniya , majalisar dinkin duniya da daukacin kasashe cewa shi dan ta’adda ne kuma ya wajaba a kawo shi ko gawarsa , alhali kuwa bai taba hada hanya ma da shi’a ba bare ya shiga .

Akwai misalai da dama da zai tabbatar mana da cewa siyasa babu wani hali mai dorewa wanda ba mamaki babbansu ya zama alakar Iran da Amurka ta inda suka raba gari wajen mas’alar makamin kare dangi , sannnan sukayi taraiya wajen kawo tashin hankali , da kawo rudu a kasar Iraki, musamman in muka san cewa Badr corps da jaishul mahdy a iran ake horasu a turosu don zubar da jini da tarwatsa garuruwan Ahlussunnah , duk su gudu don kar ya zama suna da wani matsuguni na musamman , don Shi’a su zama sune mafi yawa .

Yayin da muka so sanin zurfin Alaka tsakanin Amurka da Iran wanda masu sharhin siyasa ke ganin fuska biyu ne ga kobo daya , tana nan tun baiyanar Khomeini a matsayin dan hamaiya ga hukumar Shah . cikin Hirar da akayi da Bani Sadr (shugaban kasa na farko bayan juyin khomeini) a shirin ZIYARA KHASAH a gidan talabijin na Aljazeerah ya tabbatar cewa “ wakilan White House sunzo don ganawa da Khomeini a Neauphle le chateau inda yake gudun hijira , wanda Ibrahim Yazdi ne ya taryosu (wazirin harkokin waje a hukumar Mehdi Bazargan ) , anyi zaman da ya hada da jakadan Amurka a Tehran da Mehdi Bazargan da sauran ayoyi wanda suka dauki matakin hadin guiwa tsakanin malamai da sojoji don a samar da tsarin siyasa tsayaiye a Tehran ”, haka kuwa Khomeini ya bar Paris cikin jirgi mallakar faransa wanda aka ware masa shi da masu dafa masa baya ya sauka filin jirgin Mehrabad na Tehran 1/2/1979 abun mamaki Amurka bata tanka ba .

Zaiyi wuya wani ya gaskata cewa ba hanun Amurka a kifar da mulkin Shah saboda a daidai lokacin da hakan ya faru akwai sojojin Amurka 40,000 dubu arba’in suna aiki ma’aikatar jikin gida da tsaro da SAVAK ( Hukumar liken asiri ta a mulkin Shah ), kuma suna da tare da manyan kayan liken asiri.


Har wayau dangane da kawancen Iran da isra'ila Bani sadr cewa yayi
“ lokacinda mukai zama da sojoji ,wazirin tsaro yai bayanin cewa abun muke shiri shine sayan makamai daga Isra’ila , munyi mamakin hakan , don haka na tambayeshi , waya saka hakan? Yace : Imam Khomeini , nace wannan bazai yiyu ba , yace kasan bazan yi hakan da radin kaina ba , don haka na garzaya don ganawa da Khomeini na tambayeshi , kai ka bada dammar haka ? yace eh musulunci ma ya bada dammar yin hakan , kuma yaki shine yaki, abun ya daure mun kai , ba shakka haka ne amma ni nayi tsammanin yakinmu tsabtatacce ne , kuma jihadi shine mu yardar da yan’uwanmu su dakatar da yaki su fuskanci zaman lafiya , wannan abunda da ya wajaba ba zuwa sayo makami a Isra’ila don yakin larabawa ba, bazan yarda da haka ba , sai yace mun “ kai kana adawa da yaki , kuma dole ka yi don kaine a gurbin jagoranci ” haka babban wazirin Isra’ila Menachem Begin ya tabbatar da cewa suna taimakawa kasar Iran da makamai , shi kuma Ariel Sharon (wazirin tsaro a wancan lokacin) ya baiyana cewa suna hakan ne don raunana Iraki .

Daga cikin abunda ke razana Iran babu kamar wata kasa ta zanto tana makwabtaka da ita kuma jagororinta daliban addini ne wadanda basu bata kwakwalensu da munafunce-munafuncen siyasa ba , don wannan zai hana shigarda shi’anci a duniya , don haka ba wanda yaci moriyar ranar 11/9/2001 kamar Iran , don haka faduwar hukumar Taliban tamkar sakiya ne ga marurunta , kuwa tun tuni tana taimakawa Northern Alliance dake Mazār-e Sharīf , da tsirarun yan shi’ar kasar dake yankin Bāmiān har takai ta fara barazanar kawo sojojinta a iyakarta da Afganistan to kada Amurka kudiri aniyar yakar Taliban sai zamu ta tarda mujemu . don haka Iran ta hanzarta yarda da hukumar Hamid Karzai wanda Amurka ta kafa , shi yasa jakadan Iran a Afghanistan Muhammad Ridha Hashimy yace “ sabanin da ke tsakanin muda Al’ummar duniya tasirinsa bai baiyana a Afghanistan ba har yanzu ,kuma muna ganin lallai Afghanistan zata iya kasancewa sanfuri ga irin taimakekeniya tsakanin Tehran da Al’umar duniya ” kuma kowa zai iya fahimtar ma’anar Alummar duniya anan da cewa Amurka ake nufi , don sune jagoran yaki .

Har wayau Muhammad Abtahy a taron da sukai a Abu Dhabi
“ da badon Iran ba da Kabul da Bagadaza basu fadi ba ” .

Taraiyar Iran da Amurka kan yakar Iraki a 2003
Iran ta yi ruwa tayi tsaki wajen wannan yakin kai tsaye ko sunkuye ta hanyar Da‘wa Party da Supreme Council of the Islamic Revolution in Iraq (SCIRI), shiyasa yake a baiyane Amurka ta hada kai da shi’ar Iraki ta kuma gadar musu da mulkin Iraki su kuma sunci karensu ba babbaka kan yan sunna , suka tilasta musu kaura , sun kashe malaman masu adawa da siyasar Iran a Iraki.

Idan mai rubutu zai yi batun alakar hadin kan Amurka da Iran a Iraki (raunanniya) dole sai ya ambato wasu abubuwa kamar haka :

1- Tehran da Washinton suna da wasu cinikaiya irin tasu a boye duk da cece-kucen da suke a kafafen watsa labarai .

2- Ba kunya ba tsoron Allah Iran tayi kakagida kan al’amuran cikin gida a Iraki , don kuwa galibin masu madafan iko kasar imma yan kasar iran ne ko masu Nationality na Iran , sannan Badr Corps da Supreme Council of the Islamic Revolution in Iraq (SCIRI) suna samun horo ne daga Iran sai a watsosu Iraki don kisan gilla wannan duk Amurka tana sane da hakan , amma saboda cinikaiyarsu bata ce uffan .

Har ila yau rahoton da Robert Gates da Zbigniew Brzezinski sukayi kan Alakar kasashen biyu wanda suka samai taken Iran: Time for a New Approach , rahoton ya baiyana mahimmncin ganawa tsakanin biyu saboda dalilan siyasa da istiratijiya na alfanu ga ita Amurkan . haka rahoton da Iraq Study Group da aka fi sani da hamilton / baker shima ya ja kunnen Amurka da ta riki Iran hanu bibbiyu in har tana son kafuwa a Iraki.

Akwai dalilai masu dunbin yawa dake tabbatar da shakikancin Amurka da Iran , kuma wannan su saba kamar yadda harshe da hakori ke sabawa , ko kamar yadda Amurka da Isra’ila ake kai ruwa rana wani lokacin , ko kuma Birtaniya .

Ko kadan banyi wannan rubutun don wanke wani dan siyasa ko wata kasa daga alaka da Amurka ko Isra’ila ba , koda kuwa ta zama kasar sunnah , don kuwa kowace kasa tana da alakokinta da wadannan kasashe biyu saidai wata tafi wata , innama nufina in gwadawa wadannan masu cika bakin cewa Kasar Iran ma’asumiya ce ga abokantaka da yahudu da Nasara , in sun sani amma suke boyewa suyi adalci su fadi gaskiya, in kuwa ana yaudaransu ne to ya kamata su ringa neman sani kan abu buwanda ke gudana .

Mudai agunmu masu neman dacewa da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi , ba’a umurcemu da bin Sa’udiya ba , don haka in tayi wani katobara , baya cikin adalci ace sai mun sama mata mafita ko mu wanketa da karya da gaskiya , Don haka abunda zai daddale gaskiya tsakanin shi’a da sunnah ba abunda sarki Abdullahi ko Husni Mubarak ko kuma a daya bangaren Ahmadi Najad ko Hasan Nasrallah suka yiba , innama abunyi shine a tambatayi ko wani dan shi’a meye matsayin Sahabban Manzo tsira da amincin Allah su tabbata masa agunka , ko A’isha uwar muminai , shin meye matsayin makashin sayyidina Umar mai raba karya da gaskiya, shin abun aje Hubbarensa ne ana neman tabarruki ? . shin Abuhuraira wanda ya kiyaye hadisan manzon Allah tsira da aminci ya tabbata masa makaryaci ne kwadayaiye ? , shin da gaske wai cewa a akidarku in Sha-sauraronku yazo sai ya tashi Saiyidai Abubakar da Umar ya azabtar dasu ?.

Sannan a waiwayi Ahlussunnah a tambayesu shin Akidar ta tanadi wata darajawa da kimatawa ga Sayyidina Aliyu wanda manzon Allah ya shaida cewa yana son Allah , kuma Allah yana sonsa ? , ko Hasan da Husaine wadanda manzon Allah yace sune shugannin samarukan aljanna ? .

Naku Alkalami.