16.1.08

SHIN MATA ZA SUYI FATAN DUKIYA GA MAZAJENSU KUWA?



Wani labari da na taba karantawa kan wani nasara da ya shiga mota zaiyi kaura ya bar garinsa , bayan motar ta dau hanya sai zumbur kamar ya tuna da wani abu , ya jawo jakarsa ya bude sai ya ciro rigarsa da wando da malafa {Hat}, yayi watsi da su ta tagar mota, mamaki ya game jama'ar cikin motarnan , suka kasa hakuri suka tambaye shi, sai yayi bayanin cewa ya kauracewa matarsa ne yana so ya sake sabuwar rayuwa don haka yake yasarda duk abunda zai sa ya iya tunawa da ita .

Abun da nake so nan mu fahimta shine mutum zaiso rabuwa da duk wani abunda zai tuna masa wani kunci ko matsi ko damuwa da ya taba shiga.


To amma wani abu shine mace zata iya zama abun da za'a yasar don kar a tuna da wani yanayi da aka taba shiga na kunci musammam talauci kamar yadda wancan Nasara ya zubar da tufafinsa kuma dama Allah ta'ala cikin kurani ya kira su tufafi inda yacewa maza : [[ su tafafi ne a gareku , kuma kuma tufafine a garesu ]] suratul bakarah , ayata 187.

kamar yadda muka saba gani yayin da Allah ya budewa namiji kofofin arziki bayan ya shekara saba'in cikin talauci abunda zai fara yi shine zai tashi haikan don kauda duk abunda zai tuna masa da kwanakin talauci , don haka zai gina sabon gidan sama don kauracewa gidan kasa, ya sayi sabuwar mota don rabuwa da keke koma saiyada {sawu} ya auro sabuwar budurwa don ya bar matarsa ta fari uwar 'ya'yansa wacca suka zauna zaman hakuri da tawakkali ,

Wani mutum daya halarci wata liyafa da wani alhaji sabon kudi ya gaiyace shi yana cewa {{……bayan mun kammmala wannan liyafa wacca tana daga cikin manyan liyafofi dana taba halarta a rayuwata , abokan alhaji attajirai da 'yan siyasa suna masa bankwana da barka kan sabuwar budurwar amarya da yayi wanda shine sanadiyar wannan shagali , wasu ma sun ja motocinsu sun yi gaba sai ga wata mace marabanta da mabaraciya kadan ne tana kira ga alhazannan da su taimaketa su isar da sakonta zuwaga mai gidan , tana cewa itace matarsa shekaru arba'in da suka gabata saidai tun sanda ya fara samun kwangila a hukumar jiha da ma ta taraiya sai ya fara sauya salon mu'amala da ita , yana takalar fada don in ta mayar masa da martani ya sallame ta, hakan kuma akayi , ta kara da cewa yanzu haka wannan yaron da ke hanuna karamin dansa ne na zo karba masa hakkinsa amma masu gadi sun hana ni shiga , saboda basu santa ba, kuma dama bai taba yin masu gadi ba sai da Allah ya masa fatahi , don haka bazasu sanni ba, wannan mata ta karkare wannan bayani nata da wani matsakaicin kuka da tayi ta kokarin matse shi amma yaki . hawaye kuwa yana zuba car car daga idanunta , wasu daga cikinmu masu tausasan zukata suma suka kasa tsantsame hawayensu.}}

wannan dabi'a ta namiji yasa nayi shakkar matan aure suyi fatan Allah ya ya tarfa wa garin mazajensu nono, amma kai me ka/kika gani?


6 comments:

Anonymous said...

Lallai kam,wannan abu abun ban takaici ne ace kun wahala da mai gida amma daga baya sai yazo ya juya maki baya.
A lokacin da ya kamata ku shiga sabon rayuwa,soyayya,da nuna wa juna godiya ga arzikin da ya same ku, shi kuma adai-dai wannan lokacin ne zai ce bari ya saka maki da tsiya,sai ya koreki yaje ya auro yarinya sa'ar yarku.
Gaskiya yakamata a kiyaye asan cewa gida biyu ne in banan akwai can.

Anonymous said...

Tabbas shi yasa akce wai duk macen da tace da namiji uba,to lalai zata mutu marainiya.wasu mazan haka suke,basa iya tantance so tsakanin lokacin rashi da kuma wadatuwa.saidai kawai muyi fatan allah yasa maza sugane.domin kuwa yanzune yakama ya bude wani sabon babin soyayya da ita, amman labarin sai yazama banban

Anonymous said...

A gaskiya ina ganin rashin tunawa da wanda ya bashi wannan dukiya da kuma rashin godemai shiyasa shi ya butulcewa tsohuwar matarsa. Allah ya kyauta

T-CLassic Communications said...

Kwarai da gaske, Auwal ka taso da muhimmiyar zance a cikin rayuwan dan adam, musamman ma namiji.

Hakika kayi zazzafar tunani, mazaje diyewa sun wulakantar da matansu da suka yi zaman aure dasu a da. Wannan kuma ta kunshi yanayi da dama, saboda akwai wadansu mazaje sun sha azabar gaske a wajen matansu saboda irin talaucin da Allah ya daura musu a wannan lokacin. Do kashike, musulunci bai ce a rama mugunta da mugunta ba, amma kuma bai haramta ramako ba. Saboda irin wancan halin shiyasa wadansu maza da zarar Allah ya bude musu hanyar arziki sai kuma su fara ramakon gayya.

Amma maganar kada mata suyi wa mazan su addua'a kada a samu kudi, sam sam ba mai yiwuwa bane, domin kasan mafiya mata sun fi jin dadin arzikin mazajensu. Kaga wanda za'ayi kishiya, ana sayo mata kaya, wadansu kuma har mota suke saya wa matar.

Saboda haka, duk wanda kaga yana walakanta tsohuwar matarsa, lallai a bincika so sai da sosai, da walakin goro a miya, in kuma ba haka ba to dole ne za ayi zaman jin dadi.

Haza Wasalam.

NB
Don Allah Auwal ta yaya ka samo email dina?

alkalami alkalami alkalami said...

to malam mustafa nayi farin cikin jin ra'ayinka kan wannan makala. sannan kamar yadda ka tambate ni inda na sami email dinka , to hakika na ganshi ne ckin turakar ibrahim sheme karkashin makalar mace mutun.
na gode

Anonymous said...

I'm curious to find out what blog platform you happen to be utilizing? I'm having some small security issues with my latest blog and I'd like to find something more safeguarded. Do you have any solutions?

My website; trachtenmode riehl